fidelitybank

Jack Dorsey zai sauka daga mukamin shugaban kamfanin Twitter

Date:

A na sa ran shugaban Kamfanin Twitter, Jack Dorsey zai sauka daga mukaminsa na zartarwa a kamfanin.

Wakilin majiyar CNBC, David Faber, ya rawaito cewa, hannun jarin Twitter ya hauro sama da kashi 11 biyo bayan wallafa labarin.

A halin yanzu Dorsey ya na aiki a matsayin shugaba na Twitter da Square, kamfanin biyan kuɗi na dijital. Wani mai ruwa da tsaki na Twitter, Elliott ya nemi ya maye gurbin Jack Dorsey a matsayin Shugaba a shekarar 2020 kafin kamfanin saka hannun jari ya cimma yarjejeniya da mahukuntan kamfanin.

Wanda ya kafa Elliott kuma hamshakin attajirin nan, Paul Singer ya tambayi ko Dorsey ya kamata ya tafiyar da kamfanonin biyu, ya na mai kira a gare shi da ya sauka a matsayin Shugaba na daya daga cikinsu.

Sai dai ba a san wanda zai gaji Dorsey ba, duk da cewa, idan ya sauka, shugaba na gaba dole ne ya cimma muradan manufofin na Twitter. Kamfanin ya ce a farkon wannan shekarar yana da burin samun kudi miliyan 315 a kullum a karshen shekarar 2023, kuma a kalla ninkin kudaden shigar da yake samu na shekara a waccan shekarar.

A watan Yuni ne gwamnatin Najeriyar ta dakatar da ayyukan Twitter a kasar nan, inda ta ce ta na barazana ga kamfanoninta.

A baya dai shafin Twitter ya goge wani sako da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya wallafa game da ‘yan Kudu maso Ggabas wanda da dama daga cikin ‘yan Najeriya ke ganin bai dace ba.

Sai dai a ranar Lahadin da ta gabata, karamin Ministan Neja Delta, Festus Keyamo, ya ce kamfanin Twitter ya amince da cika dukkan sharuddan da gwamnatin Najeriya ta gindaya mata a matsayin wani sharadi na dage haramcin.

 

legit com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp