fidelitybank

Iyayen wanda ya kashe Hanifa sun tsere daga unguwar su gudun kai musu farmaki

Date:

Iyayen wanda ya kashe ‘yar shekara 5, Hanifa Abubakar; Abdulmalik Tanko, sun tsere daga gidansu saboda fargabar kai musu hari.

Politics Nigeria ta rawaito cewa, gidan dangin Tanko ya na a unguwar Tudunwada da Tudun Murtala a jihar Kano. Har yanzu ba a san inda iyayensa suke ba.

An fahimci cewa, sakamakon wannan danyen aikin na Tanko, an yi yunkurin kai wa iyayen sa hari. Wannan ci gaban ya sa iyayen mai laifin su ka gudu daga gidansu.

Tanko, mamallakin makarantar Noble Kids da ke Kano da aka kama bisa kisan Hanifa ya ce, ya kashe ta ne da maganin Bera.

Malamin makarantar wanda ‘yan sanda suka kama shi a ranar Alhamis din da ta gabata, ya amsa laifinsa ne a lokacin da yake amsa tambayoyi kan hannu a cikin wannan aika-aika.

A cewarsa, makarantar tana da rassa biyu kuma na farko  inda aka binne Hanifa  an bude ta a shekarar 2017.

Da yake bayar da cikakken bayani kan lamarin, Tanko ya ce ya tuntubi abokinsa mai suna Hashimu Isyaku da kuma wata Fatima Musa domin su yi garkuwa da yarinyar da farko amma suka kasa aiwatar da garkuwar.

Ya ce daga cikin Naira miliyan 6 da ake nema a matsayin kudin fansa, ya karbi Naira 100,000 kafin a kashe Hanifa, inda ya ce “Na yi amfani da Naira 71,000 wajen biyan ma’aikatan wani reshen.

Labarin dai ya janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta, inda da dama ke neman a yi musu adalci ba tare da bata lokaci ba.

mmm.nnn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

APC ta yi kwaf daya a zaben cike gurbin Kaduna da Jigawa

Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Jigawa ta yi...

Ba mu yarda da zaben Ghari da Tsanyawa ba – NNPP

Jam'iyar NNPP mai mulkin jihar Kano a arewacin Najeriya...

QPC ta nemi INEC ta soke zaɓen Kano

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta nemi hukumar zaɓe...

Zaɓen Kano: An kama Mutane 288 da tayar da zaune tsaye

Rudunar ƴansandan jihar Kano, ta sanar da kama mutum...

An Kama wakilin jam’iyya da Naira miliyan 25.9 na Siyan Kuri’a

Jami’an tsaro sun kama wani da ake zargin wakilin...

Farashin kayan abinci na rugu-rugu a Najeriya – NBS

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce hauhawar farashin...

Kotun Kano ta ce a kamo mata Dagacin Tamburawa

Kotun Shari’ar Musulunci da ke shelkwatar Hisbah a Kano,...

Kotu ta ƙwace motocin gwamnatin Zamfara guda 40 daga hannun Matawalle

Kotun Daukaka Kara da ke a Sokoto ta tabbatar...

A na cigaba da gudanar da zaben cike gurbi harda Kano

Kano na ɗaya daga cikin jhihohin da ake kaɗa...

Mutane 12 sun mutu a wani hatsari a Kano – FRSC

Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) reshen Kano, ta...

Masarutar Rano ta haramta aurar da Yaran da ba su kammala karatun Firamare ba

Masarautar Rano a Kano ta haramta cire yarinya daga...

Matatar Dangote za ta fara jigilar mai kyauta ga gidajen mai

Matatar man Dangote za ta fara jigilar mai kyauta...
X whatsapp