Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta shawarci jam’iyyun siyasa da su bi tsarin dimokuradiyya na cikin gida da kuma bin dokokin zabe, wajen gudanar da zabukan fitar da gwanin nasu, gabanin babban zabe.
Hukumar ta ba da wannan shawarar ne a cikin wata sanarwa da Mista Festus Okoye, kwamishinan hukumar, kuma shugaban kwamitin yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a ya fitar ranar Talata a Abuja.
Okoye ya ce, duk wata jam’iyyar siyasa da ta gaza bin tanade-tanaden dokoki wajen gudanar da zaben fidda gwani ba za a amince da su ba.
“Hukumar tana son sake jaddada cewa, dole ne jam’iyyu su bi ka’idojin dimokuradiyyar cikin gida, ta hanyar yin amfani da kundin tsarin mulki, ka’idojinsu, dokar zabe da sauran ka’idoji da ka’idojin da hukumar ta fitar.
“’Yan takararsu na mazabu 1,491 da za a gudanar da zabuka a shekarar 2023, dole ne su fito daga zaben fidda gwani na dimokuradiyya, gaskiya da inganci, daidai da tanadin sashe na 29 da 84 na dokar zabe ta 2022.