fidelitybank

Indiya ta kara shekarun aurar da mata

Date:

Gwamnatin kasar Indiya ta sanar da aniyarta na kara mafi karancin shekarun aurar da mata daga 18 zuwa 21.

Rahotanni sun ce gwamnatin ta sanar da hakan ne yayin zaman Majalisar kasar na ranar Laraba.

Yanzu haka dai a kasar, shekara 18 ce mafi karanci domin aurar da mata, 21 kuma ga maza.

Hakan dai na nufin gwamnatin za ta sauya dokar haramta aurar da Kananan yara ta 2006, da kuma yin kwaskwarima ga dokar aure ta musamman da kuma dokar aure ta addinin Hindu ta 1955.

A yayin jawabinsa na zagayowar ’yancin kan kasar na bana dai, Firaminista Narendra Modi ya bayyana bukatar yin hakan, inda ya ce, “Gwamnati ta damu matuka da lafiyar ’yan mata. Domin kare ’ya’ya mata daga matsalar yunwa, ya zama wajibi a rika aurar da su a shekarun da suka dace,” inji Firaminista Modi.

Ko a farkon wannan shekarar, Jihar Haryana ta rubuta wa, Modi wasika tana bukatar a kara shekarun aurar da mata daga 18 zuwa 21.

Aminiya ta rawaito cewa, jihar dai, wacce ke Arewacin kasar, ita ce ta fi karancin yawan mata in aka kwatanta da takwarorinsu maza a kasar ta Indiya.

natforce 
latest news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Isra’ila na zargin Canada da goyon bayan Hamas – Netanyahu

Isra'ila ta zargi Canada da taimaka wa Hamas bayan...

Rashin tallafin agaji ka iya dawo da Boko Haram a Najeriya – MDD

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta...

Yin gini a kan hanyoyin ruwa ne ya janyo ambaliyar Maiduguri – NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa da Najeriya NEMA ta...

Amnesty ta yi Allah wadai da tsare Sultan kan bidiyon lafiyar Tinubu

Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta yi...

Dalilin da ya sa na gana da Tinubu – Kofa

Ɗan majalisar tarayyar mai wakilitar Kiru da Bebeji daga...

Ba za mu jingine yajin aiki ba har sai an biya mana buƙatun mu – Ma’aikatan Jinya

Shugaban ƙungiyar ma'aikatan jinya ta Najeriya, Morakinyo-Olajide Rilwan ya...

Za a fara yi wa Dalibai gwajin kwaya kafin su shiga jami’a – NDLEA

Gwamnatin Tarayya ta ce, za ta fara yi wa...

Za mu kammala titin jirgi na Kaduna zuwa Kano a 2026 – Gwamnati

Gwamnatin Tarayya, ta ce za a kammala aikin titin...

Adadin kudaden da Liverpool ta kashe wajen daukar ‘yan wasa

Liverpool ta kashe fam miliyan 265 wajen ɗauko ƴanƙwallon...

Sunderland ta ɗauko ƴanƙwallo bakwai a kakar bana

Granit Xhaka ya zaman ɗan ƙwallo na bakwai da...

James Trafford ya sake komawa Man City daga Burnley

Mai tsaron ragar tawagar Ingila, mai shekara 21, James...

Luiz Diaz ya kammala komawa Bayern Munich daga Liverpool

Luis Diaz ya kammala komawa Bayern Munich daga Liverpool...
X whatsapp