fidelitybank

Imo: Okorocha da sirikin sa ke daukar nauyin ‘yan fashi da garkuwa da mutane – Uzodinma

Date:

Gwamnan jihar Imo, Sanata Hope Uzodimma ya zargi tsohon gwamna Rochas Okorocha da sirikinsa, Uche Nwosu da cewa sune ke da hannu wajen aikata fashi da garkuwa da mutane a jihar.

Babban sakataren yada labaran gwamnan, Mista Oguwike Nwachuku ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Talata da ya fitar ga manema labarai.

Ya ce, “Domin kauce wa shakku, Okorocha da Nwosu, musamman wadanda a ke zargi da ke hannun jami’an tsaro sun ambato su a matsayin masu daukar nauyin garkuwa da mutane da fashi da makami a jihar Imo, suna amfani da alakarsu da tsaffin tsagerun wajen aikata wannan aika-aika da laifuka.”

Uzodinma ya yi ikirarin cewa Okorocha, wanda yanzu sanata mai wakiltar Imo ta Yamma da kuma Nwosu, wanda ya rike mukamin shugaban ma’aikatansa a lokacin da ya ke gwamna, “Sun dukufa ne wajen yin amfani da hanyoyi na boye sunan su”.

A cewar sa, “Suna kuma zage-zage wajen neman bata sunan tarar jami’an tsaron da ke da alaka da gwamnan jihar Imo.”

Wannan zargin ya biyo bayan ikirarin da Mista Okorocha ya yi na cewa Mista Uzodimma na amfani da jami’an tsaro wajen gudanar da ayyukan damfara.

Okorocha ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai a makon da ya gabata cewa, “Na ga kamar an gano bakin zaren da ‘yan bindigar da ba a san ko su wanene ba su ka faru a kwanakin baya. Kuma menene (sic) ’yan bindiga da ba a san su ba? ‘Yan bindiga da ba a san ko su wanene ba yanzu sun zama ‘yan sanda daga gidan gwamnati.

“Suna samun umarni daga gwamnati karkashin jagorancin Hope Uzodinma da CSO Shaba su je su kama mutane, su kulle su yadda su ka ga dama, wani lokacin kuma ba a san inda wadannan mutane su ke ba.”

Business Hallmark ta rawaito cewa, Okorocha ya kara da cewa nan ba da jimawa ba za a iya gano abubuwan da a ka bayyana a matsayin ‘yan bindiga da ba a san su ba a jihar Imo, bayan kama Nwosu, inda ya ce kamun da Nwosu ya yi a wata coci ranar Lahadi makonni biyu da su ka gabata, ya yi karin haske kan yadda gwamnatin jihar ta Imo ta aiwatar da miyagun ayyuka ‘yan sandan da ke aiki a gidan gwamnati.

vgn news today 2021

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp