Tsohon ɗan takarar gwamna a Jihar Katsina a jam’iyar APC, Abdullahi Umar Tsauri ya ci alwashin katange ɗaukacin jihar idan ya zama gwamna.
Tsauri shine ɗan takarar gwamna a jam’iyar APGA a zaɓen 2015.
Tsauri, ya baiyana haka ne a yayin taron masu ruwa da tsaki da kuma ƙaddamar da kwamitin yaƙin zaɓen sa.
Ɗan siyasar ya ci alwashin kawo ƙarshen kashe-kashe da garkuwa da a ke yi da mutane tsawon shekaru a jihar, inda ya ce ɗaya da ga cikin dabarun samar da zaman lafiya, shine zai katange gaba ɗaya jihar.
“Zan ƙirkiro da wata dabara ta katange gaba ɗaya bodar Katsina da Zamfara da Kaduna kuma zan ɗauki ƴan vigilante 500 a kowanne bangare sa ke fama da rashin tsaron,” in ji Tsauri.