fidelitybank

Buhari ya nada Dr. Doyin Salami a matsayin mashawarci

Date:

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Dr. Doyin Salami, a matsayin babban mai ba shi shawara kan harkokin tattalin arziki.

Salami, mai shekaru 59, ya kasance shugaban kwamitin ba da shawara kan tattalin arziki na shugaban kasa (PEAC).

Salami ya kammala karatun digiri na uku a shekarar 1989 a fannin tattalin arziki a Kwalejin Queen Mary, a Jami’ar London, Doyin Salami, wanda manajan darakta ne kuma shugaban kasuwancin a KAINOS Edge Consulting Limited.

Ya kasance memba na Adjunct Faculty a makarantar kasuwanci ta jihar Legas, (LBS), Pan-Atlantic, inda kwanan nan ya sami matsayi Senior Fellow/ Associate Professor.

A na sa ran babban mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tattalin arziki zai yi jawabi a kan dukkan batutuwan da su ka shafi tattalin arzikin cikin gida tare da gabatar da ra’ayoyi a kansu ga shugaban kasa.

Har ila yau, zai sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa a cikin ƙasa da na duniya, abubuwan da ke faruwa tare da samar da martanin manufofin da suka dace.

A cewar wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya fitar, Salami zai bunkasa tare da ba wa shugaban kasa shawara kan manufofin tattalin arzikin kasa, domin samar da kwanciyar hankali a fannin tattalin arziki, inganta ci gaba, samar da ayyukan yi, da kawar da talauci da dai sauransu.

A halin yanzu, Buhari ya na da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin tattalin arziki, Adeyemi Dipeolu wanda ke aiki a ofishin mataimakin shugaban kasa. An nada Dipeolu a shekarar 2015.

legitnew

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Mun ceto tsohuwa Æ´ar shekaru 80 daga masu garkuwa – Ƴansanda

Rundunar Æ´ansandan jihar Jigawa, ta ce ta ceto wata...

APC na taron kasu ruwa da tsaki

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya za ta gudanar da...

Matatar ÆŠangote ta sake karya farashin fetur

Kamfanin Dangote da ya mallaki matatar mai ta Dangote...

Idan Isra’ila ta kai mana hari Amurka ce – Iran

Ministan harkokin wajen ƙasar Iran ya ce, gwamnatin Tehran...

Kotu ta daure mai kiwon Akuya bayan ta cinye shukokin gwamnatin Kano

Wata kotun majistare da ke Kano ta daure wasu...

‘Yansanda sun dakile yi garkuwa da mutane a Katsina

Rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ta dakile wani yunkurin...

‘Yansanda sun dakume ‘Yan Fashi uku a Kano

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu ‘yan...

Jarumar Nollywood ta zama sojan ruwar Amurka

Fitacciyar jarumar nan ta Najeriya Grace Bassey wacce a...

Na yi takaicin barin Ancelloti daga Real Madrid – Carvajal

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Real...

Mu na shirin yin kawancen jam’iyya – PDP

Majalisar dattawa ta jam'iyyar PDP, ta bayyana shirin jam'iyyar...

Ana zanga-zanga a Binuwai sakamakon harbe Dalibi dan shekara 23

Wata zanga-zanga ta barke a Makurdi, babban birnin jihar...

A na cigaba da farautar Fursunonin Osun da suka tsere

Hukumar gyaran hali ta Najeriya (NCoS) ta ce, ta...
X whatsapp