Mahaifin yarinyar da aka kashe tare da binne ta a jihar Kano, Malam Abubakar, ya shaida wa BBC Hausa cewa, ƴarsa Hanifa yarinya ce mai haba-haba.
Malam Abubakar na wannan jawabin ne a lokacin da jami’an ‘yan sandan Kano suka samu nasarar kama malamin su da ake zargi da kashe Hanifa.
Ya ce“Kullum fuskarta Hanifa cikin annuri ba ta da wata matsala, kuma mutane da dama da suka san ta za su shaida hakan.
“Hanifa yarinya ce da duk wanda ya san ta a unguwa makwabta da dangi ya san cewa tana da basira da hazaƙa, ba wanda take so kamar babanta, kuma yanzu ga halin da ta rasu a ciki,” a cwewarsa.
Sai dai ya ce ya yi imanin cewa abun da ya faru jarraba ce daga ubangiji. ”Shi dama ubangiji ya na da hanyoyin jarrabarsa da abubuwa da yawa, domin haka wannan ma jarabawa ce” .
”Magana ta ƙarshe da na yi da ita ce wadda na yi da ita ranar da za a sace ta, ta zo za ta tafi makaranta mahaifiyarta ta ce Hanifa ba ki yi addu’a ba, ta ce na yi, ta sake yi tana cewa ‘Bismillahi Tawakkalt Alallah’, tana yi da ƙarfi don ta ji cewa ta yi ɗin, ina ce mata to Hanifa kin yi, na yadda kin yi yanzu, ta tafi ta je tana sallama da mahaifiyarta, tana ce mata tun da za ki tafi kasuwa idan kin je ki taho min da alewar madara ina son zan yi sadaka da hannuna,” a cewar Malam Abubakar.
Ya ce, lokacin da ya samu labarin an kama mutumin da ya sace ta ɗin ya ji daɗi, bisa tsammanin cewa zai nuna wurin da ya ɓoye ƴarsa, amma daga baya sai ya ji abun da ya saɓa da hakan.
Ya kuma shawarci iyaye su ƙara zage dantse wajen kula da ƴaƴansu, sannan a ci gaba da addu’ar Allah ya ba da zaman lafiya mai ɗorewa.