Matasan yankin Dakata Kawaji a jihar Kano, sun fusata tare da kokarin cinna wuta tare da kona makarantar marigayiya Hanifa wadda aka yi garkuwa da ita aka kuma kashe ta.
Alkibila ta rawaito cewa, yunkurin matasan bai samu nasara ba, duk da sun kona tayoyi tare da tare titin yankin.
Tuni dai jamiāan ‘yan sanda mota 5 suka halacci wajen, domin dakile aikata barna.
Duk da matasan sunci alāwashin kone makarantar a daren ranar Alhamis, hakar su ba ta cimma ruwa ba.
Yanzu haka wanda ake zargi da kashe ta malamin makarantar su, ya tabbatarwa da ‘yan sanda cewa, da hannun sa ya dauko ta Babur din Adaidaita Sahu, ya kuma bata maganin Bera ta sha sann

Wannan ya biyo bayan sace wata yarinya yar shekaru 5 mai suna Hanifa da take makarantar da malamin su kuma mai makarantar ya yi tare da kashe ta.