fidelitybank

Gasar Kwalliya: Shatu Garko ta mayar da martani a kan kambun ta

Date:

Wacce ta lashe gasar Miss Nigeria gasar kwalliya ta mata kyau ta 2021, Shatu Garko, ta mayar da martani kan sukar da a ka yi mata game da halartar gasar kwalliya ta bana.

A kwanan baya Garko, wadda ‘yar Kano ce, ta zama ‘yar takara na farko da ta fara sanye da hijabi da ta lashe kambun da a ke so tun bayan da a ka fara gasar a shekarar 1957.

Duk da haka, kasancewarta a gasar ta ci gaba da haifar da cece-kuce, saboda addininta na Musulunci.

Da ta ke magana a wata hira da BBC Pidgin, matashiyar mai shekaru 18 ta caccaki masu sukan ta ta na mai cewa “Yan Najeriya na son yanke hukunci da kan su”. A cewar Shatu Garko.

Sabuwar Miss Nigeria ta kuma musanta ikirarin da wasu mutane ke yi na cewa ta biya, domin ta zama zakara a gasar.

“Gaskiya ’yan Najeriya suna son yin hukunci a kan mutane. Jama’a da dama sun ce shugaban kasa ne ya biya ni domin in samu rawanin, wasu kuma sun ce gwamnan jihar ya biya ya bani rawani. Akwai kuma wadanda su ka ce iyayena sun biya Miss Nigeria, amma hakan ba gaskiya ba ne,” inji ta.

Da ta ke magana kan ikirarin Hisbah, Garko ta bayyana cewa har yanzu ba a gayyace ta ba, amma ta sha samun kalamai masu zafi daga mutane.

Sai dai samfurin hijabi, ta bayyana cewa har yanzu ba ta damu da sukar da a ke mata ba, ta kara da cewa babu wani abu da za ta iya yi game da kambun.

“Babu wanda ya kira ni amma na sami maganganu da yawa da cewa ‘Na kasance tsirara’, ‘Ina yin abin da bai dace ba,” inji Shatu.

vgn news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp