fidelitybank

Ganduje ya yi ayyukan da za yaba masa – Fashola

Date:

Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya yabawa gwamna jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje kan tallafin da gwamnatin jihar ke baiwa ayyukan gwamnatin tarayya a jihar.

Ministan ya yi wannan yabon ne a yayin ziyarar ban girma da ya kai wa gwamnan yayin da ya kai ziyarar duba ayyukan gwamnatin tarayya a jihar.

A cewar Fashola, ya na jihar ne da sauran abubuwan da zai shiga cikin shirin matasa na jam’iyyar APC na kasa da aka shirya yi a Kano a ranar 27 ga watan Janairu.

Ya ce, “Abu na biyu na ziyarar tasa shi ne duba dukkan ayyukan da gwamnatin tarayya ke gudanarwa da suka hada da shirin samar da gidaje da hanyoyin da ake ginawa a Kano da kewaye.

“Dole in godewa mai girma Gwamna bisa irin hadin kan da ma’aikatar ta samu daga Gwamnatin Jihar Kano a karkashin ikon ku. Na tabbata ayyukanmu a Kano da kewaye zai yi wahala idan ba tare da hadin kan da kuka ba mu ba. Ina mika godiyar ma’aikatar mu da ta gwamnatin tarayya.

“Daya daga cikin wuraren da muka fara jin hannun zumuncin gwamnatin jihar Kano, shi ne a bangaren shirin samar da gidaje na matukan jirgi na kasa. Shekaru da yawa baya, mun sami damar samun fili a tsakiyar birnin don shirin.

“Ba wannan kadai ba, mun sami damar kammala kashi na daya da biyu na ayyukan, an kuma ba mu filayen da zai ba mu damar fadada zuwa kashi na uku. Na zo wurin domin ganin abubuwa da kaina, kashi biyu na farko sun shirya domin fara aiki,” in ji Fashola.

Ya bukaci mazauna Kano da su yi rajistar rukunin gidajen ko dai ta hanyar siya ko kuma su samu gidajen haya.

daily 
post news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp