fidelitybank

Fasinjojin Azman Air a Kano sun yi zanga-zanga a kan sauke tashin su

Date:

Daruruwan fasinjojin jirgi na Azman Air da safiyar Talata sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da matakin da aka dauka na dakatar da tashi daga Kano zuwa Legas da karfe 7:00 na safe.

DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa, ba a sanar da fasinjojin sokewar ba, har sai da ‘yan mintoci kadan da lokacin hawan jirgin ya yi.

Basu gamsu da sokewar ba, fusatattun fasinjojin suka tattaru a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, MAKIA, inda suka nufi ofishin jirgin saman Azman da ke kan titin Zariya, Kano domin bayyana kokensu.

Wasu daga cikin fasinjojin da suka gudanar da zanga-zangar sun koka kan yadda suke tafiya Legas, domin hada jiragen da za su je Landan, Masar, Dubai, Ghana da sauran wurare saboda rashin lafiya.

A halin da ake ciki, wani injiniya a kamfanin jirgin ya shaida wa wakilin DAILY NIGERIAN bisa sharadin sakaya sunansa cewa, ba zato ba tsammani na jirgin ya faru ne sakamakon wani gyara da ba a shirya yi ba aka kuma sauya lokacin tafiyar ta su.

A cewarsa, kamfanin ya lura da matsalar tsaro a cikin jirgin da aka shirya zai tashi da misalin karfe 4:00 na safe, inda ya kara da cewa, hukumar ba za ta iya yin komai ba, illa soke jirgin domin a gyara matsalar.

Sai dai ya ce an warware matsalar ta yadda wasu daga cikin fasinjojin suka amince a mayar da kudaden, yayin da wasu kuma suka zabi sauya jadawalin jiragen.

latest news in nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp