Kasar Saudiyya ta gargaɗi al’ummarta cewa, duk wanda aka kama da yaɗa labaran kanzon Kurege a shafukan sada zumunta zai fuskantar ɗaurin shekara biyar tare da tara mai yawa.
Lamarin na zuwa ne bayan soke wani casu da aka yi a birnin Riyadh ya jawo rahotannin cewa an ci zarafin wasu mata da ke kan hanyar komawa gida.
Wasu daga cikin matan sun faɗa wa BBC fargabarsu ta bayyana abin da ya faru a shafukan zumunta bayan faruwarsa.
Sai dai shugaban sashen nishaɗantarwa na ƙasar ya yi fatali da iƙirarin nasu, har ma ya yi musu ba’a a dandalin Twitter.
Casun wanda aka tsara rukunin mawaƙa na K-Pop da Stray Kids za su gwangwaje a ranar 14 ga watan Janairu, an soke shi ne ana dab da farawa saboda rashin kyawun yanayi. Hakan ya jawo wasu ‘yan kallo sun sha wahala wajen komawa gida.
Daga nan ne kuma rahotanni suka fara ɓulla a shafukan zumunta cewa wasu yara mata sun ɓace da kuma yin gargaɗin lalata da su. Nan take aka fara ƙirƙirar maudu’ai a shafukan zumunta don nuna fargaba.
Babu wani tabbas game da haƙiƙanin abin da ya faru.