An dage wasan da Burnley za ta yi da Tottenham a filin wasa na Turf Moor a gasar Premier minti 50 kafin a tashi saboda dusar kankara ta mamaye cikin filin wasan.
Ya kamata a fara wasan tun daga karfe 14:00 agogon GMT, amma duk da kokarin da ake na ganin an buga wasan an tashi da karfe 13:10.
Alkalin wasa, Peter Bankes ya ce: “Mun yi aiki tukuru, amma a cikin mintuna 10 an sake rufe filin.”
Kocin Burnley Sean Dyche, ya kara da cewa: “Dusar ta na fadowa da sauri da kuma karfi, har yanzu ya na zuba da karfi sosai.”
Kociyan Tottenham, Antonio Conte ya ce “Akwai dan takaici, saboda mun shirya mu taka leda, amma a lokaci guda ina ganin mahukunta sun yanke shawarar da ta dace, domin ceto lamarin  ‘yan wasa da magoya baya.”