fidelitybank

Dole mu tantance Tinubu idan ya na son komawa jam’iyyar mu – SDP

Date:

Shugabancin jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) ya fitar da wasu sharudda na karbar wasu ‘yan siyasa masu niyyar tsayawa takara a zaben 2023 a kan dandalin jam’iyyar.

Da yake magana a wani taron manema labarai a Abuja, mukaddashin shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Cif Supo Shonibare, ya bayyana cewa dole ne a tantance ‘ya’yan jam’iyyar APC da masu son tsayawa takara.

Sai dai ya bayyana cewa duk ‘yan takarar za su iya karbar fom din tsayawa takara daga sassan jihohinsu ko kuma daga cibiyar gudanarwa da ke Abuja.

Shonibare ya bayyana cewa,binciken da suka yi ya nuna cewa jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu ba dan jam’iyyar SDP ba ne, kuma shi ma bai samu fom din tsayawa takarar shugaban kasa na jam’iyyar ba.

“Batun Asiwaju Bola Tinubu, a karo na karshe da na duba, Asiwaju Bola Tinubu ba dan jam’iyyar Social Democratic Party ba,” in ji Shonibare.

“Na duba jerin sunayen ne saboda jerin sunayen mambobin jam’iyyarmu kamar yadda INEC ta bukata, tuni Sashen Jihohinmu suka mika mana a Abuja. Kuma babu sunansa a jerin sunayen ‘ya’yan jam’iyyar mu a jihar Legas. Abin da zan iya cewa ke nan kan shugabancin SDP. Shi ba dan jam’iyyar SDP ba ne.”

assu today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

‘Yansanda sun kwace iko da sakatariyar PDP a Abuja

A yayin da ake ci gaba da takun-saka kan...

Iran ta na da ‘yancin yin Nukiliyar ta – Ravanchi

Iran ta dage kan hakkinta na ci gaba da...

Tawagar Gwamnatin Kano ta shilla Saudiyya zuwa jana’izar Dantata

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci...

Tawagar Jami’an gwamnati da Malamai sun tafi jana’izar Dantata

Wata tawaga daga gwamnatin Tarayya, ta isa ƙasar Saudiyya...

Taimakon da Dantata ya ke yi wa Al’umma tarihi ba zai manta da shi ba – Akpabio

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana alhininsa...

Gwamnan Kano ya sauya wa hukumar Wasanni suna

Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya sauya wa...

Dalilin da ya sa Wake ya karye a Najeriya – Ƙungiyar Manoma

Ƙungiyar manoman wake a kasar nan, ta bayyana amfani...

Masu shan Taba Sigari sun shiga rudani a Faransa da firgici

A yau ne sabbin dokokin hana shan taba a...

Ni da Wike tif da taya ne – Fubara

Dakataccen gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara ya ce, babu...

Za a yi jana’izar Dantata a ranar Litinin

Babban sakataren marigayi Alhaji Aminu Dantata, Mustapha Abdullahi Junaid,...

Talauci da rashin tsaro na iya barazana ga zaɓen 2027 – Rahoto

Ƙungiyar fafutikar kare haƙƙin ɗan'adam da tabbatar da dimokuraɗiyya...

Tinubu ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalan Dantata

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya aike da saƙon ta'aziyarsa...
X whatsapp