Everton ta dauki Dele Alli daga Tottenham kan kwantiragin shekaru biyu da rabi a kan kudi fam miliyan 40.
Sabon mai horas da Everton Frank Lampard, ya sanya hannu kan siyan dan wasan tsakiya Alli, kuma ya yi imanin zai iya sake gina sana’ar da ta tsaya cak a ‘yan shekarun nan.
Dan wasan mai shekaru 25, wanda ya bugawa Ingila wasa sau 37, ya buga wasanni shida karkashin Antonio Conte, bayan zuwan dan kasar Italiya a watan Nuwamba.
Za a biya fam miliyan 10 na farko na kudin sayan sa bayan wasanni 20 da ya buga.