fidelitybank

Da Dumi-Dumi: An yi wa shugaban kasar Burkina Faso juyin mulki

Date:

Jami’an tsaro sun kama shugaban kasar Burkina Faso, Roch Marc Christian Kabore.

A ranar Litinin din ne dai sojojin da suka yi kaurin suna suka bayyana cewa, gwamnatinsa ta gaza ba su goyon baya a yayin wani kazamin harin da aka kai musu.

Jaridar Dailypost ta rawaito cewa, an ji karar harbe-harbe tun a daren Lahadi a kusa da gidan Kabore, da ke birnin Ouagadougou, babban birnin kasar na Burkina Faso.

Rahotanni sun bayyana cewa, Kabore na tsare a wani sansanin soji, yayin da manyan wurare ke ganin an samu karin jami’an soji da motoci masu sulke.

Daruruwan sojoji rufe da fuska an jibge su a ginin kafafen yada labarai na gwamnati, RTB, wanda ke nuni da cewa, za a iya yada labarai nan ba da jimawa ba.

An yi imanin cewa, tattaunawar ta wargaje tsakanin masu yunkurin juyin mulkin da ministan tsaro, Janar Barthelemy Simpore.

Lamarin dai na nufin juyin mulkin da aka yi a Afirka, wanda ya fara a shekarar 2020, ya bazu zuwa shekarar 2022.

Masu fafutuka a Mali, karkashin jagorancin Kanar Assimi Goita, sun tsige shugaba Ibrahim Boubacar Keita a watan Agustan 2018.

A watan Satumban 2021, manyan sojoji a Guinea, karkashin jagorancin Kanar Mamady Doumbouya, sun hambarar da shugaba Alpha Conde.

Sudan ta yi juyin mulki a watan Oktoban 2021 bayan yunkurin farko da bai yi nasara ba. Sojojin sun maido da ikon farar hula bayan wata yarjejeniya amma har yanzu suna cikin gwamnati.

legit.ng.news.

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United...

Gwamnatin Tinubu ta jefa al’umma fiye da miliyan 150 cikin tsananin talauci – NLC

A daidai lokacin da gwamnatin shugaban Najeriya Bola Ahmed...

Sojoji sun ce sun hallaka Æ´an Ta’adda 60 a jihar Borno

Dakarun sojijin Operation HaÉ—in-Kai sun ce sun kashe Æ´an...

Zan cigaba da jajircewa a kan rantsuwar da na yi ta kujera ta – Fubara

Gwamnan jihar Ribas da aka dakatar, Sim Fubara, ya...

Ambaliya ya kashe Mutane a jihar Neja

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, mutane da dama sun...

Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamnan Edo

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta amince da...

An kashe aÆ™alla mutum 10,217 a mulkin Tinubu – Amnesty

Wani bincike da ƙungiyar Amnesty International ta fitar kwanan...

Gwamnati ba ta tausayin Talaka – Atiku

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben...

Elon Musk ya ajiye aikin da Trump ya naÉ—a shi

Hamshaƙin attajirin nan Elon Musk ya sanarda aniyarsa ta...

‘Yar Najeriya ta haihuwa a aikin Hajjin bana

Wata mata da ta je aikin hajji daga jihar...

Rashin nadi da jinkiri ne ya kawo rashin nasarar mu a kakar 2024/2025 – Kano Pillars

Kungiyar Kano Pillars ta yi imanin cewa jinkirin shirye-shiryen...
X whatsapp