fidelitybank

A iya hukunta Abdulmalik a gaban bainar jama’a – Aisha Buhari

Date:

Uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta bukaci da a hukunta mai makarantar nan Abdulmalik Muhammad Tanko, wanda ya yi garkuwa da wata dalibar da ke karkashin kulawar sa Hanifa Abubakar tare da kashe shi.

Tanko, wanda shi ne mallakin makarantar Noble Kids Academy, dake Dakata a Kano ya amsa laifin yin garkuwa da ita tare da kashe karamar yarinya da gubar bera.

Uwargidan shugaban kasar ta bayyana a shafinta na Instagram da aka tabbatar, domin nuna goyon bayanta ga kiran da fitaccen malamin addinin musuluncin nan na Kano, Malam Abdalla Gadon Kaya ya yi, wanda ya bukaci a hukunta Tanko a bainar jama’a.

Aisha Buhari ta rubuta “Muna bayan mallam.” A cewar ta.

A cikin wani faifan bidiyo, Gadon Kaya ya tuhumi shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje da cewa “A kashe Tanko kamar yadda ya kashe Hanifa.”

Gadon Kaya ya ci gaba da cewa, ran Tanko bai fi na kananan yara ba, domin haka a kashe shi a fili.

Haka kuma masu makarantu masu zaman kansu sun yi kira da a gurfanar da abokin aikinsu wanda ya kashe ta.

An yi ta cece-ku-ce game da kisan Hanifa, inda # JusticeForHanifa ke yawo a kafafen sada zumunta a kwanakin nan.

An yi garkuwa da Hanifa Abubakar a ranar 4 ga Disamba, 2021, kuma an kashe shi bayan makonni biyu; An tsinci gawarta bayan binne ta a harabar makarantarta ta.

‘Yan sanda sun kama Tanko ne a lokacin da yake kokarin karbar kudin fansa Naira miliyan 6 da ya nema daga iyayen karamar yarinya Hanifa.

latest news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Za mu É—auki matakin hana sake faruwar kisan mutane – Gwamnatin Filato

Gwamnatin jihar Filato ta jaddada aniyarta ta É—aukar mataki...

Babu barazanar tsaro a Abuja – Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ce, babu wata barazanar a babban...

Isra’ila za ta mayarwa da Iran martani duk da tsagaita wuta

Ministan tsaron Isra'ila, Katz ya bayyana cewa, ya ba...

Ba mu kai wa Isra’ila hari ba – Iran

Kafar watsa labarai ta Iran ta ruwaito gwamnatin ƙasar...

Duk da faduwar farashin mai NNPCL ya kara farashi

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya ƙara farashin...

Duk wasu Æ™awayen Amurka za su É—anÉ—anar kuÉ—arsu – Iran

Rundunar dakarun juyin juya halin Iran ta fitar da...

Iran ta mayar da martani kan sojojin Amurka dake Qatar

Kafofin yaɗa labaran Iran sun bayyana cewa ƙasar ta...

Faransa ba ta goyon bayan Amurka na kifer da gwamnatin Iran – Barrot

Ministan harkokin wajen Faransa ya ce, ƙasarsu ba ta...

Kotu a Kano ta É—aure masu satar Yara

Babbar kotun jihar Kano da ke zamanta a Miller...

Ba wata hujja da Amurka za ta kai wa Iran hari – Rasha

An gudanar da tattaunawa tsakanin shugaban Rasha Vladimir Putin...

Tinubu ya miÆ™a saÆ™on ta’aziyya ga mutanen Kano da Kaduna da Borno

Shugaba Bola Tinubu ya yi Alla-wadai da kisan wasu...

Amurka ta tafka babban kuskure – Iran

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya yi Alla-wadai...
X whatsapp