Hukumar kwallon ƙafa ta Ivory Coast da ke karbar baƙuncin gasar 2023,FIF ta sanar da korar kocin ƙasar lokacin da ake tsaka da gudanar da wasannin gasar Afcon.
“An kawo ƙarshen kwantaragin koci ean-Louis Gasset da mataimakinsa Ghislain Printant saboda ba sa kawo sakamakon mai kyau,” in ji sanarwar FIF.
An yi wa tawagar dukan kawo wuƙa inda Equatorial Guinea ta doke ta da ci 4-0 a wasan ƙarshe na rukunin A a ranar Litinin.
Ba shi ne koci na farko da aka kora ba ana tsaka da gasar ghana ma ta kori na ta mai horaswar a ranar Talata, Tanzaniya ma ta kori Adel Amrouche a matsayin kocinta.
Shi kuwa kocin Gambia Tom Saintfiet ajiye aikinsa ya yi bayan cire ƙasar da aka yi a matakin rukuni.