fidelitybank

Da sani na Isra’ila ta kai hari Iran – Trump

Date:

Shugaban Amurka, Donald Trump ya bayyana cewa, yana sane da hare-haren da Isra’ila ta kai kan Iran kafin ta kai amma ya jaddada cewa babu hannun Amurka a ciki.

Trump ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da Fox news dangane da hare-haren.

Ya kuma maimaita cewa yana fatan Iran za ta ci gaba da tattaunawa da Amurka domin rage barazanar shirinta na makaman nukiliya.

“Iran ba za ta mallaki bam na nukiliya ba, kuma muna fatan komawa teburin tattaunawa.” in ji shi a hirarsa da tashar talabijin na Fox News.

Ya ƙara da cewa, “Akwai wasu daga cikin shugabannin Iran da ba za su sake dawowa ba,” yana nuni da cewa Amurka ta tabbatar da mutuwar wasu shugabannin Iran a harin.

Trump ya ce gwamnatinsa ta tuntubi wata muhimmiyar ƙasa kawarta a Gabas ta Tsakiya kafin a kai harin don sanar da su, sai dai bai ambaci sunan kasar ba.

nigeria newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Najeriya na cece-kuce dangane da rasuwar Muhammadu Buhari

Mutuwar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta bar cece-kuce ga...

Da Ɗumi-Ɗumi: Kashim Shettima zai rako gawar Muhammadu Buhari zuwa Najeriya

Tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya rasu. Ya rasu ne...

Ina Tinubu ya ke ya ɓata ba bayani – ADC

Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC, ta soki Shugaba,...

Koriya ta Arewa za ta ba Rasha ƙarin sojoji domin yaƙin Ukraine

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya yi...

Jam’iyyar ADC alheri ce ga siyasar Najeriya – Femi Gbajabiamila

Shugaban ma'aikata na fadar gwamnatin Najeriya, Femi Gbajabiamila ya...

Tinubu na yunkurin tauye hakkin ma’aikata – Atiku

Tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa a Najeriya, Atiku Abubakar, ya...

Trump ya lafta wa ƙasashen Tarayyar Turai da Mexico harajin kashi 30

Shugaban Amurka Donald Trump ya lafta wa ƙasashen ƙungiyar...

INEC ta ce za ta buɗe shafin intanet domin rajistar sababbin jam’iyyu

Huhukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC, ta ce nan...

EFCC na neman Rabi’u Auwalu Tijjani ruwa a jallo a Kano

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin...

An gano musabbabin hatsarin jirgin saman Indiya

Masu bincike sun bayyana sakamako na farko-farko game da...

Amurka ta haramta wa shugaban kasar Cuba shiga kasar

Amurka a karon farko ta ƙaƙaba takunkumi kan shugaban...

An kashe mutum 6,800 tare da sace 5,402 a 2025 Najeriya – Rahoto

Alƙaluma na nuna cewa an kashe mutum dubu shida...
X whatsapp