fidelitybank

Buhari ya yabawa Ganduje a kan addu’o’in zaman lafiya

Date:

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yabawa gwamnatin jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, bisa shirya taron yi wa kasa addu’a.

Shugaba Buhari wanda ya samu wakilcin wakilcin ministan ma’aikatar ayyukan gona, Alhaji Mustapha Baba Shahuri.

Ya ce, an shirya taron a dai-dai lokacin da ya da ce, inda ya ce dama addu’a ce kadai hanyar maganin matsalolin kasar nan.

ya bayyana hakan ne yayin taron yiwa Kasa addu’a wadanda Gwamnatin Jihar Kano ta Shirya da nufin Samun saukin Matsalolin tsaro da ake fuskanta a Wasu jihohin Kasar nan.

A jawabinsa gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ce, an shirya taron ne domin kaskantar da kai ga Allah tare da rikonsa ya kawowa Najeriya saukin matsalolin da a ke fuskanta.

Ya kuma bada tabbacin duk shekara gwamnatin za ta rikka shirya taron kamar yadda shugaban kasa ya bukata, tare da yin roko ga Sheikh Dahiru Usman Bauchi da ya amince da bukatar gwamnatin Kano na gudanar da mauludin Shehu Ibrahim Inyas na kasa a Kano.

Gwamna Ganduje ya godewa duk mahalatta taron musamman Khalifan Tijjaniya na Duniya Sheikh Sidi Ali Bil Arabi da ‘yan tawagar sa bisa halartar Kano da su kai, domin yi wa Najeriya addu’o’in samun zaman lafiya.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana lokacin taron Addu,a da gwamnatin Kano ta shirya a filin wasa na Sani Abacha da ke nan kano.

Da ya ke nasa jawabin sa, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, bayan ya yabawa gwamna Ganduje,ya kuma bada tabbacin za su kawo Mauludin Sheikh Ibrahim Inyas na wannan shekarar Kano kamar yadda Gwamnan ya roka.

Sheikh Dahiru Bauchi ya kuma yabawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari, kan yadda ya ke kokari wajen inganta tsaro a kasar nan.

 

 

 

 

tribune

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp