fidelitybank

Buhari ya umarci Super Eagles su kawo kofin AFCON Najeriya

Date:

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tattauna da ‘yan wasan Super Eagles, gabanin wasansu na zagaye na biyu da kasar Tunisia a gasar cin kofin nahiyar Afrika da aka shirya gudanarwa a daren yau Lahadi.

Da yake magana ta hanyar bidiyo daga fadar shugaban kasa ta Villa, Abuja, shugaban ya tattauna da Koci Augustine Eguavoen, da kyaftin Ahmed Musa da Amaju Pinnick, shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF), da sauran su.

Shugaba Buhari da ya ambaci sunayen biyu daga cikin ‘yan wasan, Kelechi Iheanacho da Moses Simon, ya bukaci Super Eagles da su ci gaba da faranta wa ‘yan Najeriya rai, ba wai kawai ta lashe wasan zagaye na biyu ba, amma a karshe su dauke kofin.

Shugaban ya ce: “Ku na yi wa Najeriya alfahari. Ku na cin nasara. Da fatan za a ci gaba da yin nasara. Gwamnatin Tarayya ta na ba ku goyon baya, kuma na ce na gode wa dukkan ma’aikata da ’yan wasa..Da fatan za a ci gaba da yi wa kasa alfahari.” In ji Buhari.

Shugaba Buhari, a cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya fitar, ya yaba wa ministan wasanni da ci gaban matasa, Sunday Dare bisa kyakkyawan aikin da yake yi.

Da yake mayar da martani, Koci Eguavoen ya ce; “Mun ji dadin yadda mai girma shugaban kasa Buhari ya tattauna da mu a safiyar yau. A madadin ‘yan wasa da ma’aikatan kungiyar, ina so in ce mun gode sosai”. A cewar Eguavoen.

legit latest news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

INEC za ta fitar da sabbin ƙa’idojin duba sakamakon zaɓe

A shirye-shiryen da take yi gabanin babban zaɓen Najeriya...

Isra’ila ta amince da sharuɗɗan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Isra'ila ta amince...

Buhari ba zai taɓa cin amanar Tinubu ba – Garba Shehu

Tsohon babban mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai...

Mutane 207 ne suka mutu a ambaliyar Neja – NSEMA

Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta...

Jiga-jigan jam’iyyar PDP za su sauya sheƙa don tunkarar APC a 2027

Wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP da suka hada da tsohon...

Za a ƙaddamar da jam’iyyar hammaya da za ta tunkari APC

Gamayyar jam'iyyun adawa a ranar Talata, ta amince da...

Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram Takwas a jihar Borno

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun kashe aƙalla...

Sauya sunan Kwaleji a Oyo ya fusata Dalibai

Ɗaliban kwalejin fasaha ta Ibadan sun gudanar da zanga-zanga...

Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan Dantata

Tawagar gwamnatin Kano da Jigawa sun kai ziyarar ta'aziyya...

Trump ba shi da hankali ko tunani a kan harajin sa – Elon Musk

Tsohon mai ba shugaban Amurka Donald Trump shawara kan...

Dangote ya rage man fetur lita 840

Matatar man Dangote ta rage farashin litar man fetur...
X whatsapp