fidelitybank

Bincike: An kashe sojoji 966 a shekara guda

Date:

Wani rahoto da wata cibiyar tattara bayanan sirri ta SB Morgen Intelligence ta wallafa, ta ce an kashe jami’an tsaro a Najeriya da su ka kai 966 a shekara guda.

Cibiyar ta saki rahoton ne a ranar Alhamis, bayan tattara bayanan sirrin da ta yi na hare-hare da aka kai wa jami’an tsaro daga watan Oktoban 2020 zuwa Satumbar 2021.

Rahoton ya bayyana cewar, ma’anar yaÆ™i a matsayin duk wani rikici da a ka kashe mutum aÆ™alla 1,000 saboda wannan za su iya cewa Najeriya na cikin yaÆ™i.

Zuwa yanzu babu wani martani daga hukumomin tsaron Najeriya game da rahoton kamar yadda BBC ta shaida.

AlÆ™alumman rahoton na SB Morgan sun bayyana cewa an kashe sojoji 642 da Æ´an sanda 322 a cikin hare-haren da ‘yan bindiga suka kai wa jami’an tsaro a cikin watanni 12.

An kuma kashe jami’an tsaron kare fararen hula na Civil Defence 11 na jami’an hukumar kwastan biyar da DSS biyu da jami’an shige da fice guda biyu da jami’in hukumar kiyaye haÉ—urra guda.

Rahoton ya kuma ce, na kashe a kalla ‘yan bindiga 1,989, yayin da aka kashe mayaÆ™an Boko Haram 973 sai kuma ‘Æ´an kungiyar asiri 290.

Kazalika mutum 129 ne suka mutu daga cikin ‘yan sintiri da mutum 100 daga masu fafutukar kafa Æ™asar Biafra da masu fashi da makami 99 da Æ´an bindiga masu satar mutane domin kuÉ—in fansa 88.

Sai dai rahoton bai mayar da hankali ba kan yawan fararen hula da aka kashe. Kamfanin ya ce ya mayar da hankali ne kan waÉ—anda rikicin ya shafa kai-tsaye waÉ—anda ke faÉ—a da jami’an tsaro.

Rahoton ya kuma ce alÆ™alummansa ba su shafi mutanen da aka kashe ba a harin da ya shafi na Æ´an ta’adda ko Æ´an bindiga.

 

 

 

 

 

 

 

asuu news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp