fidelitybank

NLC: Buhari ya fuskanci gagarumin zanga-zanga a 2022

Date:

Kungiyar Kwadago NLC ta gargadi shugaban kasa, Muhammadu Buhari game da shirin cire tallafin man fetur a shekarar 2022, inda ta ce matakin zai fuskanci gagarumar zanga-zanga a fadin kasar.

Kungiyar ta ce za a fara gudanar da gangamin ne ba tare da gargadi ba, idan har gwamnatin tarayya ta sanar da sabon farashin man fetur gabanin gudanar da zanga-zangar da za a yi a dukkan jihohin kasar nan.

An shirya gudanar da zanga-zangar ne a ranar 27 ga watan Janairu, 2022, kuma za ta kai ga mika wa dukkan gwamnonin jihohi 36 wasikun zanga-zangar.

Bayan haka, NLC ta ce, za a kuma gudanar da zanga-zangar kasa a Abuja a ranar 1 ga Fabrairu.

Wadannan na daga cikin kudurorin majalisar zartarwa ta kasa na kungiyar NLC da aka gudanar a gidan ma’aikata dake Abuja a ranar Juma’a.

Gwamnatin tarayya ta ce, za ta cire tallafin man fetur a shekara mai zuwa biyo bayan shawarar da asusun lamuni na duniya da bankin duniya suka bayar.

A nata bangaren, ministar kudi, Misis Zainab Ahmed, ta ce, kimanin talakawan Najeriya miliyan 40 ne za a rika biyansu alawus din sufuri na Naira 5,000 duk wata.

 

the nation news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Mu na aiki tuÆ™uru wajen daÆ™ile ayyukan ta’adda a Najeriya – Christopher Musa

Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya tabbatarwa...

Mayaƙan ISWAP sun harbe Manoma 23 a Borno

Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar mayaƙan ISWAP ta kashe...

Real Madrid ta É—auki É—an wasan baya daga Bournemouth

Real Madrid ta sanar da sayen É—an wasan baya...

Gwamnatin Kano ta haramta yin bikin Ƙauyawa da gidajen biki

Hukumar tace fina-finai a jihar Kano ta sanar da...

An kashe Æ´an Boko Haram biyar a Borno

Dakarun sojin Najeriya haɗe da wasu maharba sun daƙile...

Farashin Shinkafa zai cigaba da sauka – BUA

Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya alƙawarta...

An kashe mutane 10 a wani sabon rikici da ya ɓarke a Filato

Aƙalla mutabe 10 ne aka kashe tare da sace...

Duk da sauƙin da aka samu har yanzu Abuja na fuskantar hauhawar farashi

Duk da cewa hukumar ƙididdiga ta ƙasa NBS, ta...

Hauhawar farashi ya ragu da kaso 23.71 a Najeriya – NBS

An samu raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya daga...

Fiye da mutane 100 Makiyaya aka kashe a Jos

An ruwaito cewa an kashe wani makiyayi guda da...

Tinubu ka kori shugaban JAMB – Sowore

Dan siyasa mai fafutuka, Omoyele Sowore, ya yi kira...

Majalisa ta yi watsi da ƙudirin karɓa-karɓa

Majalisar wakilai ta yi watsi da wani ƙudirin doka...
X whatsapp