fidelitybank

Bankin kasa CBN ya rage kudin da bankuna ke cajar mutane

Date:

Babban Bankin Kasa (CBN) ya ba da umarnin a rage kuɗin da bankunan ke caza yayin cire kuɗi ta ATM da kuma tura kuɗin ta intanet tsakanin bankuna.

Matakin na ƙunshe ne cikin wata sanarawa da Chibuzor Efobi, shugaban sashen kula da tsare-tsaren kuɗi da dokoki, ya fitar ya na mai umartar bankuna da cibiyoyin kudi da su sauya tsarin.

CBN ya ce, an ɗauki matakin ne saboda a tabattar bankunan na bin sabbin tsarin da kasuwanci ke tattare da shi.

Sauyin ya shafi kudin Naira 65 da ake cazar mutum idan ya ciri kuɗi ta ATM na bankin da ba nasa ba sau uku cikin wata ɗaya, inda aka mayar da shi Naira 35.

Haka nan kuma an rage cajin aika kudi ta intanet tsakanin bankuna daga N300 zuwa N50 a matsayin mafi yawan adadin da za a caji mutum.

Akwai tsarin bin diddigin ayyukan bankunan domin tabbatar da cewa an daƙile yawan cazar mutane ba tare da amincewarsu ba.

world news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

A na neman kusan Mutane 400 da suka ɓace a ambaliyar Neja

A na ci gaba da ayyukan ceto bayan ambaliyar...

Mun bayar da hutu ranar Litinin bisa jimamin mutuwar ƴan Wasa – Gwamnatin Kano

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar...

Tun farko na shaida wa Tinubu ba zan zaɓe shi ba – Amaechi

Tsohon ministan sufuri na Najeriya, Rotimi Amaechi ya ce...

Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United...

Gwamnatin Tinubu ta jefa al’umma fiye da miliyan 150 cikin tsananin talauci – NLC

A daidai lokacin da gwamnatin shugaban Najeriya Bola Ahmed...

Sojoji sun ce sun hallaka ƴan Ta’adda 60 a jihar Borno

Dakarun sojijin Operation Haɗin-Kai sun ce sun kashe ƴan...

Zan cigaba da jajircewa a kan rantsuwar da na yi ta kujera ta – Fubara

Gwamnan jihar Ribas da aka dakatar, Sim Fubara, ya...

Ambaliya ya kashe Mutane a jihar Neja

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, mutane da dama sun...

Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamnan Edo

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta amince da...

An kashe aƙalla mutum 10,217 a mulkin Tinubu – Amnesty

Wani bincike da ƙungiyar Amnesty International ta fitar kwanan...

Gwamnati ba ta tausayin Talaka – Atiku

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben...
X whatsapp