fidelitybank

Ballon d’Or: Ronaldo ya mayar da martani mai zafi a kan kyautar

Date:

Cristiano Ronaldo ya zargi editan kwallon kafa na Faransa da yin karya bayan ya ce burin dan kasar Portugal shi ne ya yi ritaya da karin kyautar Ballon d’Or fiye da Lionel Messi.

Mai shirya Ballon d’Or Pascal Ferre ne ya yi wannan ikirarin ga jaridar New York Times.

A ranar Litinin ne Messi na Paris St-Germain ya lashe kyautar Ballon d’Or karo na bakwai, yayin da Ronaldo wanda ya lashe sau biyar ya zo na shida.

Ronaldo ya ce “A ko da yaushe ina yin nasara ga kaina da kuma kungiyoyin da na ke wakilta. Na yi nasara ga kaina da kuma wadanda suke so na, ba na cin nasara a kan wani.”

A ranar Juma’a, Ferre ya shaida wa jaridar New York Times cewa: “Ronaldo ya na da buri daya kacal, kuma shi ne ya yi ritaya da karin Ballon d’Or fiye da Messi, kuma na san hakan saboda ya fada min”.

Ronaldo ya mayar da martani a shafukan sada zumunta inda ya ce, “Pascal Ferre ya yi karya, ya yi amfani da sunana wajen tallata kansa da kuma tallata littafin da ya ke yi wa aiki. Ba abin yarda ba ne cewa mutumin da ke da alhakin bayar da irin wannan babbar kyautar zai iya yin karya ta wannan hanyar, ba tare da mutunta wanda ya taba mutunta kwallon kafa ta Faransa Football da Ballon d’Or ba. Babban burina a rayuwata shi ne na lashe kofunan kasa da kasa a kungiyoyin da na ke wakilta da kuma ‘yan wasan kasa a kasata. Babban burina a rayuwata shine in bar sunana a rubuce a cikin haruffan zinare a tarihin kwallon kafa na duniya.” Inji Ronaldo.

vanguard news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp