fidelitybank

Badaru ya bada hutu sakamakon Jigawa ta cika shekaru 31 da kafuwa

Date:

Gwamnatin jihar Jigawa ta ayyana ranar Juma’a 26 ga watan Agusta, 2022 a matsayin ranar da babu aiki domin tunawa da cika shekaru 31 da kafa jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Hussaini Ali Kila ya sanya wa hannu ga jaridar DAILY POST.

A cewar sanarwar, Gwamna Badaru Abubakar ya taya ma’aikatan gwamnati da daukacin al’ummar jihar murnar zagayowar ranar.

Sanarwar ta kuma bukaci jama’a da su yi addu’a ga jihar da kasa baki daya yayin gudanar da bukukuwan ranar.

Ya shawarci ma’aikatan gwamnati da daukacin al’ummar jihar da su yi amfani da hutun kwana daya wajen gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya ba su yanayi mai kyau, da zaman lafiya tare da yi masa addu’ar Allah ya kawo mana dauki domin ceto al’ummar kasar daga kalubalen tsaro da ke addabarsu.

An kafa jihar Jigawa daga tsohuwar jihar Kano a ranar Talata 27 ga watan Agusta 1991 da shugaban mulkin soja na lokacin, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya kafa.

naija news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Kotu ta yanke wa Matashin da ya kashe Budurwarsa hukuncin kisa

Kotun babban birnin jihar Nasarawa ta yanke wa wannan...

PDP ta yi watsi da matakin shugaban jam’iyyar da ya dauka

Kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, ya yi watsi da...

Tinubu zai sanya hannu kan sabbin dokokin haraji

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai sanya hannu kan...

‘Yan Bindiga sun kashe Sojoji a Neja

Rundunar Sojin Kasa, ta tabbatar da mutuwar wasu daga...

Kungiyoyi 110 suna bukatar mu yi musu rijista – INEC

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta tabbatar da samun buƙatu...

Majalisar dokoki na son Iran ta yanke hulɗa da hukumar sanya ido kan makamashin nukiliya

Majalisar dokokin Iran ta kaɗa ƙuri’a domin yanke hulɗa...

Ƴan sanda sun kama mutum 26 da ake zargi da hannu a kashe-kashen Benue

Sufeto Janar na ‘ƴan sanda, Kayode Egbetokun, ya bayyana...

Ba dan mun yi wa Iran barna ba da har yanzu ba ta nemi sulhu ba – Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake jaddada cewa harin...

Iran ta zartar da hukuncin kisa kan masu leken asiri

Kamfanin dillancin labarai na sashen shari'a a Iran ya...

Za mu ɗauki matakin hana sake faruwar kisan mutane – Gwamnatin Filato

Gwamnatin jihar Filato ta jaddada aniyarta ta ɗaukar mataki...

Babu barazanar tsaro a Abuja – Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ce, babu wata barazanar a babban...

Isra’ila za ta mayarwa da Iran martani duk da tsagaita wuta

Ministan tsaron Isra'ila, Katz ya bayyana cewa, ya ba...
X whatsapp