fidelitybank

Ba na tattaunawa da kowa kan komawa APC — Kwankwaso

Date:

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa bashi da wani shiri na barin jam’iyyar sa ta PDP Zuwa Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya.
Sanata Kwankwaso ya baiyana hakan ne cikin wata hira da ya yi da Gidan Rediyon  DW da ke Ƙasar Jamus.
 DW ya rawaito Sanata Kwankwaso ya na cewa a yanzu dai bashi da wata niyya ta barin jam’iyyar PDP Zuwa APC,  kamar yadda a ke ta jita-jitar zai bar jam’iyyar saboda rashin Ylyi da shi da ba a yi a jam’iyyar.
“Maganar sauya sheƙa babu ita a yanzu ɗin nan. Ba na magana da wasu mutane kan cewar kan koma APC” inji Kwankwaso.
Jita-jita ta yi ƙarfi cewa Kwankwaso zai sauya sheƙa zuwa APC kuma zai sulhunta da abokin burminsa a siyasa, Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje bayan da gwamnan ya kai masa ziyarar ta’aziyyar rasuwar ƙanin sa, Inuwa Kwankwaso.
Sai dai kuma a makon nan da mu ke ciki, sai gwamnatin Ganduje ta yi wa Kwankwason raddi kan kalaman da ya yi cewa gwamnan bai ci zaɓe ba a shekarar 2019.

news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp