fidelitybank

Artabu: ‘Yan ta’adda 38 sun mutu ciki harda ‘yan sanda 5 – ‘Yan Sanda

Date:

Akalla ‘yan ta’adda 38 ne a ke zargi an kashe yayin da jami’an ‘yan sanda biyar su ka rasa ransu a wani arangama da a ka yi da juna daban-daban a jihar Katsina a shekarar 2021.

Kwamishinan ‘yan sanda jihar Katsina, Sanusi Buba ya bayyana hakan ne yayin wani taron ‘yan jarida na musamman.

Kwamishinan wanda ya samu wakilcin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ya koka da ayyukan ‘yan ta’adda a jihar.

Ya ce “Hakika, ba shakka lokaci ne mai wahala, rundunar ta samu gagarumar nasara a kan barazanar ta’addanci, garkuwa da mutane, fashi da makami da sauran nau’ikan laifuka da aikata laifuka a jihar. Shekarar 2021 ta samu a cikin raguwar yawan laifuka a jihar idan a ka kwatanta da shekarar da ta gabata.”

“A yayin wannan artabun, an kashe ‘yan bindiga talatin da takwas (38) a fadan bindigu daban-daban yayin da jami’an ‘yan sanda biyar (5) suka biya su ka rasa ransu,” inji shi.

Kwamishinan ya ce, rundunar ta kama mutane 999 da a ke zargi da aikata laifuka 608 da a ka samu. Yayin da adadin wadanda a ka kama 874 ke fuskantar shari’a a kotunan shari’a daban-daban na jihar.

Ya kara da cewa an kama jimillar mutane 157 da a ke zargin ‘yan fashi da makami ne, sannan 145 daga cikinsu an gurfanar da su gaban kotu yayin da 12 ke ci gaba da bincikar su.

“An kama masu garkuwa da mutane sittin da biyar sannan an gurfanar da 63 a gaban kotu yayin da biyu ke kan bincike.”

Ya kuma ce,”An kama mutane 244 da a ke zargin barayin shanu ne, daga cikinsu an gurfanar da wadanda a ke zargin 230 a gaban kotu yayin da 14 ke ci gaba da bincikar su. An kwato dabbobin gida guda 1,243 wadanda su ka hada da shanu 867, tumaki 352, awaki 24 da jaki daya daga cikin mazubin”. A cewar sanarawar.

Kwamishinan ya ce an kama mutane 246 da ake zargi a cikin 195 da aka samu na fyade da kuma laifukan da suka saba wa ka’ida inda ya ce an kubutar da mutane 63 da aka yi garkuwa da su a wasu shari’o’i hudu da aka samu na fataucin bil adama da aka kai ofishin NAPTIP na jihar Kano.

assu news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp