fidelitybank

Gwamnatin Jigawa ta amince da hukuncin kisa a kan masu fyade

Date:

Gwamnatin jihar Jigawa ta amince da dokar kare hakkin yara wadda ta tanadi hukuncin kisa ga wadanda su ka yi wa kananan yara fyade.

Bisa doka, duk wanda a ka samu da laifin yi wa yarinya ‘yar kasa da shekaru 10 fyade, za a yanke masa hukuncin kisa na tilas ba tare da zabin tara ba.

Kwamishinan shari’a na jihar, Dr Musa Adamu ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a wata ganawa da manema labarai a Dutse babban birnin jihar.

Ya kuma ce“A farkon wannan shekarar ne gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya sanya hannu kan dokar hana cin zarafi da ta’addanci wadda ta tanadi hukuncin kisa ga masu fyade, amma da zabin daurin rai-da-rai. Amma a kwanan baya gwamnati ta kuma sanya hannu kan dokar kare hakkin yara wadda ta tanadi hukuncin kisa ga duk wanda ya yi wa yarinya ‘yar kasa da shekara 10 fyade”.  Inji Kwamishinan.

“A cikin jimillar adadin littafan shari’o’in, 90 sun kasance na fyade; 27 kisan gilla; luwadi ya na da 31; sacewa 18; lalata biyu; biyu 2 ayyuka na babban alfasha; ‘Yan fashi da makami guda 20 ne yayin da laifuffukan kan hanya ke da shari’a biyu.

“Ma’aikatar ta gabatar da kara tare da kare jimillar kararraki 25 a gaban kotun daukaka kara ta Kano, sannan ta kuma kammala shari’ar laifuka 83 a gaban manyan kotuna takwas da ke Birnin Kudu, Dutse, Gumel, Hadejia, Kazaure da Ringim. An sallami mutane 34 da a ke tuhuma da laifuka 49 kuma an sallame su”. A cewar Dr. Musa.

Dr Musa Adamu ya kuma yi kira da a yi amfani da na’urorin zamani domin rage jinkirin shari’ar, a cewarsa na daya daga cikin manyan kalubalen da bangaren shari’a ke fuskanta a jihar Jigawa.

punch news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Za mu ɗauki matakin hana sake faruwar kisan mutane – Gwamnatin Filato

Gwamnatin jihar Filato ta jaddada aniyarta ta ɗaukar mataki...

Babu barazanar tsaro a Abuja – Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta ce, babu wata barazanar a babban...

Isra’ila za ta mayarwa da Iran martani duk da tsagaita wuta

Ministan tsaron Isra'ila, Katz ya bayyana cewa, ya ba...

Ba mu kai wa Isra’ila hari ba – Iran

Kafar watsa labarai ta Iran ta ruwaito gwamnatin ƙasar...

Duk da faduwar farashin mai NNPCL ya kara farashi

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya ƙara farashin...

Duk wasu ƙawayen Amurka za su ɗanɗanar kuɗarsu – Iran

Rundunar dakarun juyin juya halin Iran ta fitar da...

Iran ta mayar da martani kan sojojin Amurka dake Qatar

Kafofin yaɗa labaran Iran sun bayyana cewa ƙasar ta...

Faransa ba ta goyon bayan Amurka na kifer da gwamnatin Iran – Barrot

Ministan harkokin wajen Faransa ya ce, ƙasarsu ba ta...

Kotu a Kano ta ɗaure masu satar Yara

Babbar kotun jihar Kano da ke zamanta a Miller...

Ba wata hujja da Amurka za ta kai wa Iran hari – Rasha

An gudanar da tattaunawa tsakanin shugaban Rasha Vladimir Putin...

Tinubu ya miƙa saƙon ta’aziyya ga mutanen Kano da Kaduna da Borno

Shugaba Bola Tinubu ya yi Alla-wadai da kisan wasu...

Amurka ta tafka babban kuskure – Iran

Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya yi Alla-wadai...
X whatsapp