fidelitybank

APC Kano: Buhari bai amince da wani bangare ba – Fadar shugaban kasa

Date:

Fadar shugaban kasa ta yi fatali da wata sanarwa da daya daga cikin bangarorin jam’iyyar APC reshen jihar Kano, ya yi na cewa, sun samu amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cikin wata sanarwa da babban mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar, fadar shugaban kasar ta ce, Buhari bai amince da wani bangare ba, inda ya kara da cewa wannan magana ba gaskiya ba ce.

Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasar ya amince da daya daga cikin bangarorin APC a Kano.

“Wannan ba gaskiya ba ne a fili. Wannan ba zai iya faruwa ba yayin da al’amura ke jiran shari’a daga kotuna. Don a fayyace wannan, shugaba Buhari bai amince da wani bangare ba. Goyon bayan sa na jam’iyyar APC ne a matsayin jam’iyya, hadin kai da karfi, ba na kowane bangare ba”. inji sanarwar fadar shugaban kasa.

Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa hakan na zuwa ne kasa da mako guda bayan da gwamnatin jihar Kano ta musanta rade-radin da a ke yadawa cewa gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da bangarensa na shirin sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PRP.

Wannan jita-jita ta fito ne bayan wani taro da bangaren gwamnan na APC ya yi a yunkurin da kotun Abuja ta yanke na daukaka kara kan hukuncin da kotun Abuja ta yanke kan mazabun jam’iyyar da na kananan hukumomi da a ka gudanar a gidan gwamnatin jihar Kano a Africa House a ranar Lahadin da ta gabata.

Wata babbar kotun Abuja ta kori shugabannin jam’iyyar APC na Kano masu biyayya ga gwamna Ganduje tare da ayyana shugabannin tsohon gwamnan jihar Ibrahim Shekarau a matsayin zababben shugabannin jam’iyyar a jihar.

bbc news 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar Ĉ´ansandan jihar Kaduna, sun buĈ™aci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi Ĉ™ungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban Ĉ™aramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp