Kwamishinan kananan hukumomi na Jihar Kano, Hon. Murtala Sule Garo, ya jagoranci shugabannin kananan hukumomi 44 na jihar a ziyarar ta’aziyyar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, bisa rasuwar kanin sa, Inuwa Kwankwaso.
Kwamishinan da shugabannin kananan hukumomin, wadanda su ka nuna alhininsu game da rasuwar Inuwa, sun yi addu’ar Allah ya jikan marigayin.
PlatinumPost ta rahoto cewa a baya Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kai ziyara ga Kwankwaso, inda ya jajanta wa tsohon gwamnan a madadin gwamnatin jihar da kuma al’ummar jihar.
Inuwa, wanda kani ne ga Sanata Kwankwaso ya rasu ne a safiyar ranar Litinin 20 ga watan Disamba, 2021 a asibitin koyarwa na Aminu Kano bayan doguwar jinya ya na da shekaru 64.
Ya kasance ma’aikacin gwamnati mai ritaya kuma injiniyan noma. Marigayin ya bar matarsa da ‘ya’ya mata biyu: Barr. Nafisa Inuwa da Zainab Inuwa.