fidelitybank

APC Kano: Buhari bai amince da wani bangare ba – Fadar shugaban kasa

Date:

Fadar shugaban kasa ta yi fatali da wata sanarwa da daya daga cikin bangarorin jam’iyyar APC reshen jihar Kano, ya yi na cewa, sun samu amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cikin wata sanarwa da babban mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar, fadar shugaban kasar ta ce, Buhari bai amince da wani bangare ba, inda ya kara da cewa wannan magana ba gaskiya ba ce.

Rahotanni sun bayyana cewa, shugaban kasar ya amince da daya daga cikin bangarorin APC a Kano.

“Wannan ba gaskiya ba ne a fili. Wannan ba zai iya faruwa ba yayin da al’amura ke jiran shari’a daga kotuna. Don a fayyace wannan, shugaba Buhari bai amince da wani bangare ba. Goyon bayan sa na jam’iyyar APC ne a matsayin jam’iyya, hadin kai da karfi, ba na kowane bangare ba”. inji sanarwar fadar shugaban kasa.

Jaridar DAILY POST ta rawaito cewa hakan na zuwa ne kasa da mako guda bayan da gwamnatin jihar Kano ta musanta rade-radin da a ke yadawa cewa gwamnan jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje da bangarensa na shirin sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PRP.

Wannan jita-jita ta fito ne bayan wani taro da bangaren gwamnan na APC ya yi a yunkurin da kotun Abuja ta yanke na daukaka kara kan hukuncin da kotun Abuja ta yanke kan mazabun jam’iyyar da na kananan hukumomi da a ka gudanar a gidan gwamnatin jihar Kano a Africa House a ranar Lahadin da ta gabata.

Wata babbar kotun Abuja ta kori shugabannin jam’iyyar APC na Kano masu biyayya ga gwamna Ganduje tare da ayyana shugabannin tsohon gwamnan jihar Ibrahim Shekarau a matsayin zababben shugabannin jam’iyyar a jihar.

sun news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ĉ³an Najeriya na cece-kuce dangane da rasuwar Muhammadu Buhari

Mutuwar shugaban Ĉ™asa Muhammadu Buhari ta bar cece-kuce ga...

Da ĈŠumi-ĈŠumi: Kashim Shettima zai rako gawar Muhammadu Buhari zuwa Najeriya

Tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya rasu. Ya rasu ne...

Ina Tinubu ya ke ya ɓata ba bayani – ADC

Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC, ta soki Shugaba,...

Koriya ta Arewa za ta ba Rasha Ĉ™arin sojoji domin yaĈ™in Ukraine

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya yi...

Jam’iyyar ADC alheri ce ga siyasar Najeriya – Femi Gbajabiamila

Shugaban ma'aikata na fadar gwamnatin Najeriya, Femi Gbajabiamila ya...

Tinubu na yunkurin tauye hakkin ma’aikata – Atiku

Tsohon ɗantakarar shugaban Ĉ™asa a Najeriya, Atiku Abubakar, ya...

Trump ya lafta wa Ĉ™asashen Tarayyar Turai da Mexico harajin kashi 30

Shugaban Amurka Donald Trump ya lafta wa Ĉ™asashen Ĉ™ungiyar...

INEC ta ce za ta buɗe shafin intanet domin rajistar sababbin jam’iyyu

Huhukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC, ta ce nan...

EFCC na neman Rabi’u Auwalu Tijjani ruwa a jallo a Kano

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin...

An gano musabbabin hatsarin jirgin saman Indiya

Masu bincike sun bayyana sakamako na farko-farko game da...

Amurka ta haramta wa shugaban kasar Cuba shiga kasar

Amurka a karon farko ta Ĉ™aĈ™aba takunkumi kan shugaban...

An kashe mutum 6,800 tare da sace 5,402 a 2025 Najeriya – Rahoto

AlĈ™aluma na nuna cewa an kashe mutum dubu shida...
X whatsapp