fidelitybank

An tsige shugaban kwamitin tsaro a Kazakhstan a kan zanga-zanga man fetur

Date:

Shugaban kasar Kazakhstan ya tube guda daga cikin kusa a tafiyar sa a harkokin tsaron kasar daga mukaminsa na shugaban majalisar tsaron kasar a ranar Laraba, bayan da masu zanga-zangar suka kutsa kai tare da kona gine-ginen jama’a a wani rikici mafi muni da kasar ta shafe fiye da shekaru goma ana yi.

Majalisar ministocin ta yi murabus, amma hakan ya gaza kwantar da hankulan masu zanga-zangar bayan kwashe tsawon kwanaki a na tashe tashen hankula, sakamakon tashin farashin mai a kasar da ke hako mai a tsakiyar yankin Asiya.

Wasu masu zanga-zangar sun yi ta rera taken adawa da Nursultan Nazarbayev, mai shekaru 81, wanda ya ci gaba da rike madafun iko tun bayan da ya sauka a shekarar 2019 a matsayin wanda ya fi dadewa kan karagar mulki a tsohuwar kasar ta Soviet.

Wanda ya gaji Nazarbayev, shi ne shugaba, Kassym-Jomart Tokayev, ya ce, ya karbi ragamar jagorancin kwamitin tsaro mai karfi mukamin da Nazarbayev ya rike.

Har yanzu dai a na kallon tsohon shugaban a matsayin babban jigon siyasa a Nur-Sultan, babban birnin da a ka gina da sunan sa. An yi imanin danginsa suna sarrafa yawancin tattalin arzikin kasar.

 

bbc nigeria news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Fernandes na duba yiwuwar barin Man Utd zuwa Al-Hilal

Bruno Fernandes na duba yiwuwar ficewa daga Manchester United...

Gwamnatin Tinubu ta jefa al’umma fiye da miliyan 150 cikin tsananin talauci – NLC

A daidai lokacin da gwamnatin shugaban Najeriya Bola Ahmed...

Sojoji sun ce sun hallaka Æ´an Ta’adda 60 a jihar Borno

Dakarun sojijin Operation HaÉ—in-Kai sun ce sun kashe Æ´an...

Zan cigaba da jajircewa a kan rantsuwar da na yi ta kujera ta – Fubara

Gwamnan jihar Ribas da aka dakatar, Sim Fubara, ya...

Ambaliya ya kashe Mutane a jihar Neja

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, mutane da dama sun...

Kotu ta tabbatar da nasarar Gwamnan Edo

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta amince da...

An kashe aÆ™alla mutum 10,217 a mulkin Tinubu – Amnesty

Wani bincike da ƙungiyar Amnesty International ta fitar kwanan...

Gwamnati ba ta tausayin Talaka – Atiku

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaben...

Elon Musk ya ajiye aikin da Trump ya naÉ—a shi

Hamshaƙin attajirin nan Elon Musk ya sanarda aniyarsa ta...

‘Yar Najeriya ta haihuwa a aikin Hajjin bana

Wata mata da ta je aikin hajji daga jihar...

Rashin nadi da jinkiri ne ya kawo rashin nasarar mu a kakar 2024/2025 – Kano Pillars

Kungiyar Kano Pillars ta yi imanin cewa jinkirin shirye-shiryen...
X whatsapp