Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo, ya sanar da cewa daga Litinin din wannan makon, an kawo karshen hana jama’ar jihar fita wuraren aiki da sana’o’insu a fadin jihar.
Gwamnan ya kuma sanar da cewa, gwamnatinsa ta yi wa mutanen da ke dauke da makamai afuwa, musamman wadanda ke yin kira da a raba Najeriya gida biyu, kuma a kafa kasa ta ‘yan yankin zalla.
Farfesa Charles Soludo ya sanar da haka cikin wata sanarwa, inda ya jaddada cewa, zai dawo da zaman lumana a jihar.
Wasu mayaka, wadanda mambobin kungiyar IPOB ne kungiyar da gwamnatin Najeriya ta haramta wa aiki a Najeriya, sun rinƙa kai hare-hare a jihar ta Anambra da yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.
Mambobin kungiyar na son a sako shugabansu Mazi Nnamdi Kanu.
“Mun yi ma ‘yan uwanmu wadanda ke cikin dazukan jiharmu afuwa. Ku mika mana bindigoginku, kuma ku amince mana mu taimaka muku gina rayuwa mai afani”, inji gwamna Soludo.