fidelitybank

An kashe basarake tare da kona mutane 3 cikin tawagarsa a Ogun

Date:

Wasu mutane da suka nuna ba a sani ba sabo, sun kashe wani basarake tare da kona mutum uku a cikin ’yan tawagarsa da ransu a yankin Alagodo da ke Karamar Hukumar Ewekkoro ta Jihar Ogun.

Majiyar Aminiya ta ce, wasu ’yan daba ne suka tare Oba Ayinde Odetola ne tare da abokansa, suna dawowa daga rangadi, suka kashe shi sannan suka kona abokan nasa da ransu, bayan barkewar rikicin sarautar Alagodo da ke Kasar Egba.

Majiyar ta ce, tun bayan kisan da aka yi wa basaraken da abokan nasa da misalin karfe 11 na ranar Litinin, wasu mazauna yankin suka fara kaura daga garin.

Rikicin ya kunno kai ne bayan takaddama a kan wanda za a ba wa sauratar yankin a tsakanin ’yan kabilar Ake da kuma kabilar Owu da ke zaune a yankin na Kasar Egba.

Oba Ayinde Odetola da aka kashe dai dan kabilar Ake ne a Kasar Egba, inda wadansu mazauna suke bore a kan cewa babu yadda za a ayi dan kabilarsa ya mulki masarautar saboda ’yan kabilar Owu ne ke da rinjayen al’umma.

Majiyoyi a yankin Kasar Egba sun tabbatar mana cewa ko a kwanakin baya sai da aka yi wa wani kasin Oba Otedola kisan gilla a sakamakon rikicin.

Wata ’yar uwar Oba Odetola mai suna Cif Adenike Akintade, ta ce, “A ranar Litinin da safe aka sallamo ni daga asibiti, ga shi kuma na shiga halin juyayin rasuwar dan uwana da aka kashe da misalin karfe 11 na safe.

“Ranar Asabar Mai Martaba ya kira ni, cewa in rage wasu abubuwan da nake yi saboda gajiya na ira kara min rashin lafiyata.

“A watannin baya Oba Odetola ya rasa kaninsa a rikicin; ’yan daba ne suka kashe shi, ga shi yau kuma Mai Martaba ya bar duniya.”

A ranar Litinin da dare ne dai Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya kara da cewa maharan sun kona motar basaraken bayan sun kashe shi.

Ya ce, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Ogun, Lanre Bankole tare da Mashawarcin Gwamna Dapo Abiodun, wato Olusola Subair, sun ziyarci garin domin gane wa kansu abin da ya faru.

A cewarsa, duk da cewa babu wanda aka kama a kan zargin, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar ya umarci sashen ’yan sanda masu binciken laifukan kisa da ya gudanar da bincike a kan al’amarin.

legitnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp