fidelitybank

A saki kadarorin kudaden Afghanistan – Iran

Date:

Kasar Iran ta bukaci gwamnatin Taliban da ta bude kadarorin kudaden Afghanistan da a ka toshe tun bayan da Taliban ta karbe iko da sako su.

A cewar wani kamfanin dillancin labarai na kasar, bayan ganawarsa da mukaddashin ministan harkokin wajen Afghanistan Amir Khan Muttaqi.

Ministan harkokin wajen kasar Iran, Hossein Amirabdollahian ya bayyana cewa, kadarorin kasar Afghanistan da Amurka ta toshe cewa kamata a yi amfani da su wajen gudanar da ayyukan jin kai da kuma kyautata yanayin rayuwa a Afghanistan.

Yakin da jajirtattun al’ummar Afganistan su ka yi ya nuna cewa, babu wani karfi na waje da zai iya mamaye kasar ta Afganistan kuma ya yi mulki a can,” in ji shi.

A ranar 15 ga watan Agusta ne mayakan Taliban masu tsattsauran ra’ayin Islama suka karbe iko da kasar Afganistan a daidai lokacin da sojojin Amurka da na kasashen waje suka janye, bayan shafe shekaru 20 suna goyon bayan gwamnatin Kabul da ke samun goyon bayan kasashen Yamma.

Tuni dai gwamnatocin kasashen waje suka dukufa wajen tsara yadda za su hada kai da kungiyar Taliban, domin kaucewa tabarbarewar tattalin arziki da tsaro a Afghanistan tare da kaucewa amincewa da sabuwar gwamnati a hukumance.

nnn hausa

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da É—anyen man kaÉ—anya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaÉ—a labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...

An gargadi Borno da Yobe da Jigawa su zama cikin shirin ambaliya

Akwai yiwuwar samun ambaliya a jihohin Borno, Jigawa da...
X whatsapp