Mayakan Boko Haram sun kai farmaki garin Rann hedikwatar karamar hukumar Kala-Balge a jihar Borno inda suka kashe manoma sama da 60.
Wani ganau ya shaida wa Tribune Online cewa, an samu raunukan harsasai da dama a gawarwakin wadanda suka mutu, kamar yadda ya ce har yanzu wasu manoman sun bace.
A cewar shaidar gani da ido, an yi jana’izar wadanda aka kashe a ranar Litinin bisa ga umarnin Musulunci.
“’Yan ta’addan Boko Haram a kan babura dauke da bindigu da adduna sun kewaye gonakinsu suka fara kashe su daya bayan daya,” inji ganau ya bayyana.