Rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi, a ranar Talata, ta tabbatar da kisan wani jami’in ta da wasu ‘yan bindiga suka yi masa kwanta ɓauna a zagayen bankin Union, Abakaliki, babban birnin jihar.
Wanda aka kashe, wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba, har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, ‘yan bindigar sun kashe shi ne a daren ranar Litinin, yayin da wasu ‘yan sanda biyu suka samu munanan raunukan harbin bindiga.
Rahotanni na cewa, jami’an ‘yan sandan sun tsaya suna aikin bincike a zagayen bankin Union, unguwar da bankunan suka fi yawa a cikin babban birnin jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ebonyi, CP. Faleye Olayele ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, Onome Onovwakpoyeya ya rabawa manema labarai.
Kwamishinan ya ce: “Jami’an ‘yan sandan da ke aikin tsayawa da bincike a zagayen bankin Union, yankin da bankunan ke da babban birnin jihar, sun yi artabu da ‘yan bindiga dauke da muggan makamai, wadanda ba a san inda suke ba.
“Abin bakin ciki ne, daya daga cikin jami’an ya biya farashi mai tsoka, yayin da wasu biyu suka samu raunuka kuma suna karbar magani a asibiti. Har ila yau, ’yan bindigar sun yi asarar rayuka, amma an tafi da su. ”
Kwamishinan ya sha alwashin tabbatar da cewa an gurfanar da wadanda suka kashe a gaban kuliya domin amsa laifin da suka aikata a jihar.
“Ya kamata jama’a su kwantar da hankalinsu, saboda an dauki matakan kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa,” in ji shi.
Olayele ya yi kira ga jama’a da su kai rahoton duk wanda aka gani da raunin harsashi ko kuma ya nemi a yi masa magani a jihar.