fidelitybank

Ƴan APC sun shigar da ƙara a kotu suna neman ta hana babban taron jam’iyar na ƙasa

Date:

 

 Wasu fusatattun ƴan jam’iya mai mulki, APC sun garzaya zuwa Babbar Kotun Taraiya a Abuja domin ta hana shugabancin riƙo na Mai Mala Buni shirya babban taron jam’iya na ƙasa a watan Febrairu.
Waɗanda su ka shigar da ƙarar a ranar 4 ga watan Janairu, sun haɗa da Suleiman Dimas Usman, Muhammed Shehu, Samaila Isahaka, Idris Isah, da kuma Audu Emmanuel.
Lauyan masu ƙara, Olusola Ojo, shine ya shigar da ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/3/2022.
Masu ƙarar sun ce yin babban a Febrairu taron zai saɓawa kundin tsarin dokokin APC.
Sun ƙara da cewa rashin yin zaɓukan shugabannin jam’iya na jiha a dukkanin jihohi 36 na ƙasa gami da Abuja, APC ba ta da ikon shirya taron.
Sun ƙara da cewa APC ta yi zaɓukan shugabannin jam’iya na jiha a jihohi 34, amma ba ta yi a Jihohin Anambra da Zamfara ba.
Waɗanda a ke ƙara sun haɗa da Jam’iyar APC, Shugaban Kwamitin Riƙo na APC da kuma Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC.
Kawo yanzu dai, kotun ba ta sanya ranar da za ta saurari ƙarar ba.

vgn

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Mata da kanan Yara ne Ambaliya ta daidaita a jihohi 19 – NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa, NEMA, ta...

Facebook ya ƙi amincewa da tsare-tsaren Turai na amfani da AI

Wasu muhimman tsare-tsare na dokokin Tarayyar Turai kan amfani...

Ranar 18 za a fara rajistar zabe – INEC

Hukumar zaɓe mai zaman kanta, INEC ta sanar da...

Trump ya tura jiragen ruwa na yaki masu dauke da makaman nukiliya kusa da Rasha

Shugaba Trump ya ce, ya umarci a matsar da...

Amnesty na tuhumar gwamnatin Najeriya kan bacewar Dadiyata

Ƙungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da sakacin da...

Rundunar sojin ruwa za ta kafa sansani a Kebbi

Rundunar sojin ruwan Najeriya ta bayyana aniyar kafa sansaninta...

Za afara rijistar masu zabe a Najeriya – INEC

Hukumar zaɓe ta INEC, ta ce, nan gaba cikin...

Ma’aikatan Jinya sun dakatar da yajin aiki a Najeriya

Ministan lafiya a Najeriya ya ce, ma'aikatan jinya da...

Izak ya na ɗaukar horo bayan ya dage sai ya koma Liverpool

Ɗanwasan gab ana Newcastle Alexander Isak na can yana...

Masu tsaigunta wa ƴan Bindiga ne ke haddasa kashe-kashe – Gwamnan Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta ce masu tsegunta wa ƴanbindiga...

Gwamnoni ku yi wa mutanen ƙauyika da karkara ayyuka – Tinubu

Shugaba Bola Tinubu, ya buƙaci gwamnonin ƙasar nan su...

Dino Melaye ya gudu daga PDP ya faɗa ADC

Tsohon ɗan jamalisar dattawa mai wakiltar Kogi ta Yamma,...
X whatsapp