Ƙungiyar ƙwadogo ta TUC, ta gargaɗi gwammatin tarayya da ta guji janye tallafin man fetur a daidai wannan lokaci da ta ce talakawa na cikin mawuyacin hali na matsin tattalin arziki.
Ƙungiyar na ganin idan har gwamnatin ta janye tallafin farashin man, to hakan zai ƙara wa jama’ar ƙasa ɗimbin wahalhalu da kuma matsin tattalin arziki.
Abin da kuma ita ƙungiyar ta TUC ke cewa ba za ta amince da shi ba.
A Tattaunawarsa da BBC mai magana da yawun ƙungiyar Kwamared Nuhu Toro, ya ce, babu yadda za a yi a cire tallafin ba tare da an zauna an tattauna batun cire tallafin tsakanin masu ruwa da tsaki ba.
Ya ce matuƙar aka cire tallafin man to farshinsa zai yi tashin gwauron zaɓi, abin da kuma zai shafi farashin sauran kayayyaki a ƙasar.
Kwamared Toro ya ce, cire tallafi ba shi ne mafita wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa ba.