Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya dade yana cewa Iran na kusan da kera makamin nukiliya.
Amma kuma abin da ya ki fitowa ya tabbatar wanda da yawa aka yi amanna da shi, shi ne cewa, Isra’ila tana da makamana nukiliya na kanta tun daga shekarun 1960.
Yawancin abin da kiyasin cibiyar hana bazuwar makamai ta duniya ta ce shi ne Isra’ila tana da makaman nukiliya kusan 90.
Sannan kuma kasar ba ta cikin mambobin da suke cikin yarjejeniyar duniya ta hana bazuwar makaman nukiliya.
Masu sharhi sun yi amanna Isra’ila na tafiyar da shirinta na nukiliya ne a tashar nukliya ta Dimona, wani birni da ya ke hamadar Negev.
Isra’ila tana da wata manufa ta boye magana – kuma har kullum ta ki ta tabbatar cewa tana da makaman nukiliya sannan kuma ba ta ce ba ta da su ba.