fidelitybank

Ziyarar Aiki: Buhari ya tafi kasar Turkiyya

Date:

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja zuwa birnin Santanbul na ƙasar Turkiyya, domin halartar taron haɗin gwiwa tsakanin Turkiyya da Afirka karo na uku wanda shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya zai karɓi baƙwancin sa.

Mai taimaka wa shugaba Buhari kan harkokin yaɗa labarai Malam Garba Shehu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar da safiyar ranar Alhamis a birnin tarayya Abuja.

A cewar masu shirya taron, taken sa shi ne ” Samar da ingantacciyar hadin gwiwa domin samun ci gaba da ƙaruwar arziki yayin da kuma yake da mauduin yin nazari kan haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Afirka da Turkiyya tun bayan taron ƙarshe na shekarar 2014 da aka gudanar.”

“Taron hadin gwiwa tsakanin Turkiyya da Afirka na ukun dai yana zuwa ne a daidai bayan da shugaba Erdogan ya kawo ziyarar aiki Najeriya a kwanakin baya, inda aka sanya hannu kan yarjejeniyoyi da dama a fannonin makamashi harkokin tsaro sai haƙar maadinai da maadinan ruwa duk domin ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu.”

“Shugaban na Turkiyya a ziyarar da ya kawo Najeriya, ya tabbatar da aniyarsa ta gaggauta faɗaɗa harkokin kasuwancin da ke tsakanin kasashen biyu zuwa dala biliyan biyar, kuma tawagar Najeriya za ta yi amfani da damar taron da za a yi a Istanbul domin inganta haɗin gwiwa da sauran abokan hulɗar kasuwanci, ƙarin damar kasuwanci da zuba jari a kasar.”

Sanarwar ta kuma ce, a na sa ran taron zai samar da ƙa’idoji da alƙibilar haɗin gwiwa da ƙasashen Afirka a cikin shekaru biyar masu zuwa.

Shugaba Buhari zai samu rakiyar uwargidansa Aisha da ministocin da suka haɗa da na harkokin waje Geoffrey Onyeama da na Tsaro Manjo Janar Bashir Magashi mai ritaya da Ministan babban birnin tarayya Abuja Mohammed Bello da na Lafiya Osagie Ehanire sai na Noma Mohammed Abubakar da na Masana’antu Ciniki da Zuba Jari Adeniyi Adebayo.

Sauran sun haɗa da, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya da babban Daraktan hukumar leƙen asiri ta ƙasa Ambasada Ahmed Rufa’i.

sun newspaper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp