fidelitybank

Zub da Jini: Zuwa ga shugabannin hukumomin tsaro – Arewa Media Writers

Date:

Ƙungiyar Marubutan Arewa “Arewa Media Writers” ta aikewa shugabannin hukumomin tsaron Najeriya Saƙonnin halin da Al’ummar Arewa ke ciki.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta ɗauki matakin gaggawa, donmi kawo ƙarshen matsalolin rashin tsaron da ya yi muni a yankin Arewa.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Comr Abba Sani Pantami ne ya aikewa manema labarai, inda kungiyar ta turawa shugabannin hukumomin tsaron Najeriya sakonnin halin da al’ummar Arewa suke ciki na taɓarɓarewar tsaro, musamman a ƴan kwanakin nan.

Haka zalika ƙungiyar ta buƙaci gwamnatin ƙasar da ta tashi tsaye kan taɓarɓarewar tsaron da yayi muni a yankin Arewa dama ƙasar Najeriya baki ɗaya.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne, a cikin takaddun ƙorafi da ta turawa hukumomin tsaron mai ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar na ƙasa Comr Abba Sani Pantami, inda ƙungiyar ta bayana irin takaici da jimamin halin da al’ummar Arewa suke ciki, na rashin zaman lafiya, rashin kwanciyar hankali, ga kuma talauci da tsadar Rayuwa da al’ummar yankin suke ciki.

Ga wani sashi na saƙon da ƙungiyar ta turawa hukumomin tsaron;

“Mun yi imanin cewa kuna da kayan aiki don kawo ƙarshen waɗannan matsalolin, amma abin takaici ba mu ga wani sakamako mai kyau ba har yau. Domin magance waɗannan matsalolin, dole ne gwamnati ta ƙara yawan jami’an tsaro akan jami’an da muke da su, tare da samar da guraben ayyukan yi da dama ga matasanmu. Akwai buƙatar matasanmu su kasance masu ilmi musamman waɗanda ke zaune a yankin da babu makarantu, asibitoci, ruwa, hanyoyi da sauransu. A ƙarshe, muna buƙatar ɗaukar matakin gaggawa don kawo ƙarshen matsalolin”.

Sanarwar ta ci gaba da cewa,”Muna son zaman lafiya da adalci wanda zai iya haifar da ingantacciyar rayuwa ta al’ummarmu a dukkan jihohin Arewa da Najeriya baki ɗaya. Arewa Media Writers” za ta ci gaba da ƙoƙarin kawar da duk wasu labaran ƙarya da ka iya kawo matsala a wurin yaƙi da ƴan ta’addan tare da cigaba da wayarwa al’umma kai domin samun ci gaba da haɗin kai da cikakken haɗin kan Al’ummar mu. Mungode da fahimtar sakonmu”. A cewar Arewa Media Writers.

nigeria peace corps

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

JAMB ta amince da maki 150 mafi ƙanƙanta don samun gurbin karatu a jami’o’i

Hukumar shirya jarrabawar shiga Jami'o'i ta Najeriya (JAMB) ta...

ASUU ta dakatar da yajin aikin da ta fara

Ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta Najeriya, ASUU da dakatar yajin...

Masu haɗakar ADC na ɓaɓatu ne saboda rashin gwamnati – Radda

Gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Umar Radda ya yi...

Ba ruwan Biri da gada a makamin Nukiliya – Shettima

Mataimakin shugaba Najeriya Kashim Shettima ya ce ƙasar za...

An kashe Mutane 70 a jihar Filato

Rahotonni daga jihar Filato na cewa ƴanbindiga sun kai...

Ambaliya ta kashe mutane 100 a Amurka

Hukumomi a jihar Tesxas da ke Amurka sun bayyana...

Tsohon Ministan kuma jigo a PDP ya koma ADC

Tsohon ministan harkokin ‘yan sanda kuma sau uku a...

Trump ya caccaki Elon Musk

Shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki tsohon mashawarcinsa, Elon...

Dalilin da ya sa Kwankwaso ya ki shiga jam’iyyar hadaka – Galadima

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...

Obi ba zai taba zama shugaban kasa ba – Wike

Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce, tsohon ɗan takarar...

Ƴansanda sun kama ƴan Ghana 19 da aka yi safararsu a Najeriya

Rundunar ƴansandan Najeriya ta kuɓutar da wasu ƴan Ghana...

Benue da Edo da Bayelsa na fargabar balewar madatsar ruwan Kamaru

Gwamnatocin jihohi uku na cikin shirin ko-ta -kwana, sakamakon...
X whatsapp