Gwamna jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ce, ba zai bata lokaci ba, wajen sanya hannu kan aiwatar da hukuncin kisa ga wadanda suka yi kisan gillar da aka yi wa yarinya ‘yar shekara biyar Hanifa Abubakar.
Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar jaje ga iyalan yarinyar da aka kashe a Dakata Kawaji tare da mataimakinsa, Dr Nasiru Yusuf Gawuna da shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar, Labaran Abdul Madari da sauran manyan jami’an gwamnati a ranar Litinin.
Ya ce,“Zan bi dokar da kundin tsarin mulki ya tanadar a matsayina na gwamnan Kano na amincewa da hukuncin kisa a yanayin da kotu ta yanke kan masu laifin. Muna da kwakkwaran tabbaci daga kotun da ke tafiyar da lamarin cewa, za a yi adalci, ba za mu yi jinkiri ba,” in ji shi.
Da yake tabbatar da cewa, “Duk wanda aka samu da wannan danyen aiki, shima zai fuskanci kisa ba tare da bata lokaci ba. A matsayinmu na gwamnati, mun riga mun fara aikin.”
“Tsarin mulkinmu ya tanadi cewa, idan aka yanke hukuncin kisa, ikon mulki ne na gwamna ya amince a aiwatar da hukuncin kisa. Ina tabbatar muku da haka, ba zan bata koda dakika daya ba. A gaggauta gudanar da shari’a, gwamnati za ta kula da iyalan marigayiyarmu Hanifa mai albarka.” A cewar Ganduje.
Ganduje ya kuma ce gwamnatinsa za ta yi wani abu a kan makarantun da bala’in ya shafa.