Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PRP, Kola Abiola, ya bayyana kwarin gwiwa na lashe zaben 2023 a Najeriya.
Da yake magana a ranar Laraba a Abuja a sakatariyar jam’iyyar PRP ta kasa, Abiola, ya ce, kamar yadda mahaifinsa, Cif MKO Abiola ya yi nasara a zaben shugaban kasa na 1993, yana da kwarin guiwar samun nasara a zaben shugaban kasa na 2023.
A cewarsa, dole ne matasan kasar su kasance a shirye, domin samun sauyi na gaskiya wanda shi ne abin da yake bayarwa, ya kara da cewa yana shirin tafiyar da gwamnati mai dunkulewa.
Abiola ya bayyana hakan ne bayan ya karbi takardar shaidar cin zabe a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PRP.
Ya ce, “Ban shiga jam’iyyar PRP ba saboda ina neman wata kafa. Na shiga jam’iyyar PRP ne bayan na yi bincike. Na shiga ne saboda na yarda da akidarta. Ba za a yi zagon kasa daga tsakani ba domin ba mu ci komai ba a baya.