Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta ce, a shirye ta ke ta gudanar da zaben gwamna mai inganci a jihar Ekiti.
Da yake magana a ranar Talata yayin wata hira da gidan Talabijin na Channels cikin shirin Sunrise Daily, Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Ilimin Zabe na INEC, Festus Okoye, ya ce, hukumar za ta tura na’urar tantance masu kada kuri’a (BVAS) a zaben ranar 18 ga watan Yuni.
Okoye wanda ya bayyana cewa tuni shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya je jihar ta Kudu maso Yamma, ya bayyana cewa masu ruwa da tsaki za su sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a ranar Laraba.
“A yi sa ran gudanar da zaben (gwamnati) mai kyau a jihar Ekiti,” in ji shi.
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa ya je Ekiti makonni biyu da suka gabata kan tantance shirye-shiryen da aka yi.