fidelitybank

Zamu dawo da ma’aikatan jinya da likitoci masu aiki a waje – Gwamnati

Date:

Ministan Lafiya dakta Osagie Ehanire, ya ce, gwamnatin tarayya na wani shiri domin maido da likitoci da ma’aikatan jinya ‘yan asalin Najeriya da ke aiki a ƙasashen waje, tare da maida su aiki a jami’o’i da asibitocin ƙasar nan.

Yayin da yake jawabi a wajen gabatar da nasarorin da ma’aikatun gwamnatin tarayya suka samu ƙarƙashin wannan gwamnati ranar Talata a Abuja babban birnin ƙasar, ministan ya ce ya fahimci yadda ƙwararrun likitoci ke bariin ƙasar.

Ministan ya ce da yawa daga cikin likitoci da ma’aikatan jinya suna ganin kamar ba a biyansu ladan aikin da suke yi kamar yadda ya kamata.

Mista Ehanire ya ce gwamnatin tarayya na ƙoƙarin magance matsalar ta hanyar inganta yanayin aikin likitocin.

Ya ƙara da cewa matsalar ƙarancin likitoci matsala ce da ta shafi duniya baki-ɗaya, ba Najeriya kaɗai ba.

Ya ci gaba da cewa ”A wani zama da muka yi da ministan lafiya na ƙasar Gambiya ya yi min ƙorafi game da yadda likitoci ke barin ƙasar”.

”Sannan kuma na zanta da hukumomin Birtaniya waɗanda suma suka sanar da ni cewa mafi yawan likitocin ƙasar na tafiya Canada da New Zealand inda ake biyan albashi mai gwaɓi, dan haka suke buƙatar ƙarain likitoci a ƙasarsu, sannan haka lamarin yake a Masar da Turkiyya”.

punch news paper today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp