Jam’iyyar New Nigeria People’s Party NNPP, ta ce, babban zaben 2023 zabi ne tsakanin neman ‘yancin dimokradiyya na gaskiya ko kuma bautar siyasa.
Dan takarar gwamnan jihar Jigawa a karkashin jam’iyyar NNPP, Malam Aminu Ibrahim Ringim ne ya bayyana haka a karshen mako a lokacin da yake kaddamar da shirin jam’iyyar gabanin babban zaben 2023.
Ya ce, gazawar alkawura da wahalhalun da gwamnatocin baya suka kai wa al’ummar jihar Jigawa musamman jam’iyyar PDP da kuma gwamnatin APC mai barin gado, ya jefa ‘yan kasa da jihar cikin halin kunci.
A cewarsa “Wannan yanayi na son zuciya ba tare da wani dalili ba, ya bar jama’a suna sha’awar samun sauyi da kuma samun sabon shugabanci da gwamnati, wanda babbar jam’iyyarmu, NNPP za ta samar don sake mayar da jihar da jama’arta don girma.”
“Saboda haka ina amfani da wannan dama wajen wayar da kan al’ummar jihar Jigawa da su yi amfani da karfin kuri’unsu bisa ga hankali wajen kwato jiharmu da al’ummar kasa baki daya daga kangin siyasa da ke tafe da su ta hanyar damka wa al’umma aikin gwamnati. NNPP”
“Kada gyada ta rude ku don musanya ‘yancinmu na dimokuradiyya da kuma ikon sarrafa albarkatun gama gari don zuriya”
Mista Ringim ya yi nuni da cewa, gwamnatin NNPP a jihar Jigawa za ta maido da daidaito tare da bullo da tsare-tsare masu hade da juna wadanda za su dawo da martabar dan Adam da mutuncin jama’a da kuma amanar masu mulki.