Babban sakatare Janar na kungiyar NATO, Jens Stoltenberg, ya shirya wani taro na musamman na jakadun kasashen kawance da manyan jami’an kasar Rasha a mako mai zuwa a daidai lokacin da bangarorin biyu ke neman tattaunawa, domin hana barkewar yaki a tsakanin kasashen Ukraine.
Da ya ke firgita da yadda sojojin Rasha ke ci gaba da yi a kan iyakar kasar Ukraine,
Kawancen sojojin kasashen yammacin duniya sun shafe watanni suna neman taron kungiyar tsaro ta NATO da Rasha, amma taron ya yi kamari bayan takaddama da su ka samu tun a watan Oktoba.
Taron majalisar, tsarin da ake amfani da shi wajen tattaunawa tun shekara ta 2002, zai gudana ne a Brussels a ranar 12 ga watan Janairu, bayan da jami’an Amurka da na Rasha za su gudanar da tattaunawar tsaro a ranar 10 ga watan Janairu a Geneva.
Babban jami’in diplomasiyyar tarayyar Turai, Josep Borrell, ya tashi zuwa Ukraine a ranar Talata domin yin wata ziyarar kwanaki biyu, domin nuna goyon bayansa ga kasar Ukraine, mai burin shiga kungiyar da NATO.
Rueters ta rawaito cewa, a cikin shirye-shiryen diflomasiyya na mako mai zuwa, ministocin harkokin wajen NATO za su gudanar da taron kallo na gani ga ka na bidiyo a ranar Juma’a da karfe 13:00 agogon GMT, karkashin jagorancin Stoltenberg.
Russia na son ba da garantin cewa NATO za ta dakatar da fadada ayyukanta na gabas da kuma kawo karshen hadin gwiwar soji da Ukraine da Jojiya, wadanda ke da takaddama kan yankuna da Rasha.